Sojoji sun kama Ifeanyi Eze Okorienta, wanda aka fi sani da “Gentle de Yahoo”, ɗaya daga cikin manyan shugabannin ƙungiyar IPOB da ke neman ɓallewa daga ƙungiyar.
Rundunar ta ce an cafke shi tare da ƙwace bindigogi ƙirar Turai, alburusai, da kuma kayan sawa na sojoji da ’yansanda.
- Ya Kamata A Kiyaye Nasarorin Da Aka Cimma A Shawarwarin Sin Da Amurka
- NECO Ta Saki Sakamakon Jarrabawar 2025
Jami’an tsaro sun bayyana kama Eze a matsayin babban koma-baya ga IPOB, musamman ga sashen ƙungiyar da ke amfani da makamai a yankin Kudu Maso Gabas.
Wannan lamari ya faru ne ’yan makonni bayan wata kotu a Finland ta yanke wa wani jagoran IPOB, Simon Ekpa, hukuncin ɗaurin shekara shida a gidan yari bisa laifin ta’addanci.
IPOB ta jima tana aikata ayyukan ta’addanci a yankin Kudu Maso Gabas, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp