Dakarun rundunar soji ta 93 da ke karkashin rundunar sojin Nijeriya ta 6, sun yi nasarar cafke wata mata da ake zargi da garkuwa da mutane, lokacin da take kokarin karbar kudin fansar wani da aka yi garkuwa da shi a jihar Taraba.
Haka kuma rundunar ta damke wani dan bindiga da ya shahara wajen safarar makamai da alburusai, yana sayar da su ga masu aikata miyagun laifuka a jihar da sauran sassan Nijeriya.
- Ina Da Labarin Sirri ‘Yan Bindiga Za su Kawo Mun Farmaki – Gwamna Dikko Raɗɗa
- ‘Yan Bindiga Sanye Da Hijabi Sun Kashe ‘Yan Sanda 2 A Katsina
Bincike ya gano matar da ake zargin mai suna, Janet Igohia, ta auri wani fitaccen mai aikata laifuka wanda shi ne shugaba na biyu bayan Marigayiya Hana Terwase, da sojoji su ka kashe a shekarun baya.
Da yake karin bayani ga manema labarai, Kakakin rundunar, Laftanar Oni Olubodunde, ya ce “sojojin da ke aiki da sahihan bayanan sirri kan ayyukan dillalan makamai, su su ka kama Joshua Dutse Idah, mai shekaru 45.
“Sojojin sun bi sawun sa, wanda hakan ya sa aka kama shi a garin Ibbi, lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Kaduna, a wata karamar mota kirar Volkswagen Sharon, mai lamba Rivers SKN-390AA.
“Da aka yi masa tambayoyi, ya amsa cewa zai je jihar Katsina ne domin kawo bindigogi kirar AK-47 wanda aka biya shi wani bangaren kudin Naira 300,000.
“Bayan binciken da suka yi masa kan motar, sojojin sun gano bindigar PK 1 da harsashi na musamman 399 mm da 7.62 da kuma mujallun AK-47 guda 3,” in ji Oni.
Haka kuma kakakin rundunar ya ce rundunar ta cafke Janet Igohia, da ake zargi da garkuwa da mutane mai shekaru 31, bayan ta karbi kudi naira miliyan daya da rabi (1.5), domin biyan kudin fansa ga wani da aka sace a yankin Chanchangi da ke karamar hukumar Takum.
Ya ce Janet Igohia, ta bayyana cewa “ta auri Voryor Gata wani fitaccen mai laifi kuma tsohon shugaba na biyu ga marigayi Gana Terwase.