Dakarun sojojin Nijeriya a jihohin Filato da Zamfara sun kubutar da wasu mutane hudu da aka yi garkuwa da su tare da kashe wani dan ta’adda.
A wata sanarwa da daraktan hulda da jama’a na rundunar sojin kasar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya fitar, ya ce, sojojin da aka tura karamar hukumar Jos ta Kudu ta jihar Filato sun ceto wata Misis Rosemary Jekpe a kauyen Rafinbuna da ke karamar hukumar Bassa a jihar, bayan sun yi musayar wuta da masu garkuwa da mutane.
- Gwamnan Katsina Ya Raba Fiye Da Naira Miliyan 470 Ga Wadanda Ta’addancin ‘Yan Bindiga Ya Rutsa A Jihar
- Tsadar Rayuwa: Gwamnatin Kaduna Za Ta Kashe Naira Biliyan 11.4 Wajen Bayar Da Tallafi
Ya ce, an yi garkuwa da matar ne a gidanta da ke Abuja Layout, Bukuru Low Cost Housing a karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar Filato.
Ya ce, sojojin sun kuma kai wani samame kan wani da ake zargi da aikata laifuka a kauyen Zamtip da ke karamar hukumar Wase a jihar Filato, bayan samun bayanan sirri.
Sanarwar ta kara da cewa, a yayin samamen da sojojin suka yi, sun cafke daya daga cikin masu laifin, yayin da wani kuma a yunkurinsa na tserewa kar a kama shi, ya kashe kansa.
A wani samame da aka yi a jihar Zamfara, rundunar sojojin a wani kiran gaggawa da aka yi musu, cewa, wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu mutane Uku a wajen kauyen Kwatarkwashi da ke karamar hukumar Gusau.
Ya ce, sojojin sun yi artabu tare da fatattakar ‘yan bindigar, lamarin da ya tilasta musu sakin mutanen ukun da suka yi garkuwa da su, inda nan take sojojin suka ceto su.