Dakarun Sojin Nijeriya sun daƙile yunƙurin harin ‘yan bindiga tare da ceto fasinjoji shida a kan titin Wukari-Kente da ke ƙaramar hukumar Wukari a Jihar Taraba.
Lamarin ya faru ne a ranar 27 ga watan Afrilu, 2025, bayan samun kiran gaggawa daga Shugaban Ƙaramar Hukumar Wukari, wanda ya sanar da harin da aka kai wa wasu matafiya.
- Ranar Ma’aikata: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Alhamis A Matsayin Hutu
- Wang Yi: Neman Sulhu Da Ja Da Baya Riba Ne Ga Masu Son Cin Zali
Sojojin da ke zaune a sansanin Wukari sun yi gaggawar zuwa wajen da abin ya faru.
A cewar wata sanarwa daga Kyaftin Olubodunde Oni, mai magana da yawun Runduna ta 6, sojojin sun isa waje da abin ya faru, inda suka tarar da wata mota ƙirar Toyota Hilux tsaye a bakin hanya.
Jim kaɗan bayan haka, mutane shida suka fito daga cikin daji cikin ƙoshin lafiya, inda suka bayyana cewa su ne fasinjojin motar.
Sun ce suna tafiya daga Yola zuwa Lafia ne lokacin da wasu mutane da ake zargin ‘yan fashi ko masu garkuwa da mutane ne suka kai musu hari, lamarin da ya sa suka tsere zuwa daji don tsira rayukansu.
Sojojin sun taimaka wajen gyara tayar motar sannan suka tabbatar da cewa fasinjojin sun ci gaba da tafiyarsu cikin tsaro.
Shugaban Runduna ta 6, Birgediya Janar Kingsley Uwa, ya yaba wa sojojin bisa saurin ɗaukar mataki da kuma tsayin daka kan aiki.
Ya kuma buƙaci jama’a da su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro haɗin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai a kan lokaci domin taimakawa wajen yaƙi da laifuka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp