Sojoji sun hana mayaƙan ISWAP kai hari a yankunan Banki da Bula Yobe, da ke Jihar Borno.
Waɗannan yankuna na magidanta sama da 10,000 da suka dawo gida bayan shekaru da dama suna gudun hijira saboda ta’addanci.
- Nau’o’in Jirage Uku Sun Kammala Sauka Da Tashin Farko Bisa Taimakon Majaujawar Maganadisu A Jirgin Dako Na Fujian Na Kasar Sin
- Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Bayyana Ra’ayin Kasar Kan Rikicin Falasdinu Da Isra’ila
Mayaƙan sun kai hari a ranar 18 ga watan Satumba, 2025, da nufin tilasta wa jama’a barin gidajensu.
Amma sojojin ƙasa tare da goyon bayan rundunar sojin sama ƙarƙashin Operation HADIN KAI sun yi nasarar fatattakar su.
Majiyoyin sojoji sun bayyana cewa dakarun da ke Banki da Bula Yobe, sun tsaya tsayin daka wajen kare mata, yara da tsofaffi.
Haka kuma sun tabbatar da cewa manoma da suka koma gonakinsu kwanan nan sun samu kariya.
Babu wanda aka sace ko ɗaya, yayin da jama’ar yankin ke ci gaba da zama lafiya.
A ranar 19 ga watan Satumba, Birigediya Janar Ugochukwu Unachukwu, wanda shi ne muƙaddashin kwamandan rundunar sojojin 7 Division, ya kai ziyara Banki don yaba wa sojoji kan jarumtar da suka nuna.
Ya ce ‘yan ta’addan sun yi mummunan rashi kuma ya tabbatar wa jama’a cewa rundunar sojojin Nijeriya za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyi.
Sai dai rundunar ta tabbatar da cewa wani soja ya rasa ransa yayin kare mutanen, yayin da wasu suka ji rauni.
Sojojin sun ce wannan shaida ce ta jajircewar rundunar wajen tabbatar da zaman lafiya da kare ‘yan Nijeriya da suka koma gidajensu bayan gudun hijira.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp