• English
  • Business News
Tuesday, October 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sojoji Sun Daƙile Harin Ƴan Ta’adda, Sun Kashe Wasu Da Yawa A Borno

by Abubakar Sulaiman
5 months ago
Sojoji

Dakarun Sojojin Nijeriya na Operation Haɗin Kai sun kashe tarin ‘yan ta’adda tare da ƙwato makamai daban-daban yayin da ƴan ta’addan suka kai hare-haren da basu yi nasara ba a sansanonin Sojoji a garuruwan Buratai da Mallam Fatori, dake ƙananan hukumomin Biu da Abadam na jihar Borno.

A wata sanarwa da Mataimakin Daraktan hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojoji, shalƙwatar Rundunar Operation haɗin Kai, Kyaftin Reuben Kovangiva ya fitar, ya ce Sojojin ƙasa da haɗin gwuiwar ɓangaren jiragen sama na OPHK ne suka daƙile harin.

  • Bam Ya Kashe Mutane 9 A Wata Tashar Motoci Da Ke Borno 
  • Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda Da Dama A Wani Sabon Hari Da Suka Kai Sansanin Sojoji A Borno

Kovangiva ya ce ‘yan ta’addan sun kai hari da asuba, ranar Alhamis 5 ga Yuni, 2025, a yankin Buratai, inda suka so su kutsa sansanin Sojoji ta hanyoyi daban-daban. Amma dakarun sun mayar da martani cikin gaggawa da buɗe wutar harbi mai ƙarfi, tare da tallafin jiragen yaƙi na sama da suka baiwa Sojojin ƙasa kariya.

Sojoji

Ya bayyana cewa, zuwa yanzu an gano gawarwakin ‘yan ta’adda da dama da kuma tarin makamai daban-daban.

LABARAI MASU NASABA

NLC Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Don Biyan Buƙatun ASUU Da Sauran Ƙungiyoyi 

’Yansanda Sun Kama Ɗan Fashi Sanye Da Kayan NYSC A Enugu

A wani cigaba makamancin haka, dakarun Mallam Fatori suma sun daƙile wani yunƙurin hari daga ‘yan ta’adda da suka zo ta wurare daban-daban.

Ya ce bayan sa’o’i na musayar wuta, dakarun sun bi ‘yan ta’addan da suka tsere, inda suka hallaka da dama, wasu kuma suka gudu da raunukan harbin bindiga. An kuma kwato muggan makamai da dama kamar bindigogi AK-47, da bindigar kakkaɓo jirgi (RPG), da sauran kayayyakin yaƙi. Yanzu haka Sojojin na ci gaba da sintiri a yankin, tare da goyon bayan jiragen sama da na leƙen asiri.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

NLC Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Don Biyan Buƙatun ASUU Da Sauran Ƙungiyoyi 
Manyan Labarai

NLC Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Don Biyan Buƙatun ASUU Da Sauran Ƙungiyoyi 

October 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta
Labarai

’Yansanda Sun Kama Ɗan Fashi Sanye Da Kayan NYSC A Enugu

October 21, 2025
Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu
Manyan Labarai

Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu

October 21, 2025
Next Post
Gwamnatin Tarayya Za Ta Tallafa Wa Yekuwar Rigakafin Cutar Ƙyandar Jamus

Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka

Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka

October 20, 2025
An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole

An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole

October 20, 2025
Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar

Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar

October 20, 2025
Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu

Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu

October 20, 2025
Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan

Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan

October 20, 2025
Ƙungiyar Ƙwadago Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Ta Sasanta Da ASUU

Ƙungiyar Ƙwadago Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Ta Sasanta Da ASUU

October 20, 2025
Gina Kasar Sin Ta Dijital Na Kara Gaba Zuwa Sabon Matakin Amfani Da Basira

Gina Kasar Sin Ta Dijital Na Kara Gaba Zuwa Sabon Matakin Amfani Da Basira

October 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.