Yunkurin da wasu tawagar ‘yan ta’adda suka yi na kafa sansani a jihar Neja ya gamu da turjiya yayin da sojoji suka sake fafatawa da su a kusa da dajin Allawa.
LEADERSHIP ta tattaro cewa al’ummar kananan hukumomin Shiroro da Munya da suka fi fama da bala’in a ‘yan watannin da suka gabata sun fara samun sauki.
An tattaro cewa baya ga tsauraran hare-haren da sojoji ke kai wa dajin da ke daura da Birni Gwari a jihar Kaduna, Mamakon ruwan sama ma ya kara muzguna wa ‘yan ta’addan wajen gudanar da ayyukansu cikin walwala a dajin.
An tattaro cewa ‘yan ta’addan na da sansani a Goron Dutse kusa da Birnin Gwari inda daga nan ne suka fito domin kai farmaki a Jihar Neja amma a wani taro da suka yi a Kurebe sun yanke shawarar maida sansaninsu zuwa jihar.
Majiya mai tushe ta bayyana cewa ‘yan ta’addan suna cin karansu ba babbaka a Unguwan Baushe da Akambu da Kanon Machi da Unguwan Kumallo a kan titin Birnin Gwari, sun yi kokarin bi ta Jelako da Ga-gafada domin tserewa harin soji a jihar Kaduna.
Don haka, su ma jami’an soji a Jihar Neja suka sake fatattakar ‘yan ta’addan da dakile yunkurinsu na kafa sansani a Jihar.