Rundunar Sojin Nijeriya ta kashe ‘yan bindiga sama da 80 tare da kone baburansu 45 a Jihar Katsina.
Wannan na kunshe ne ciki wata sanarwa da rundunar sojin saman Nijeriya (NAF), ta fitar a ranar Litinin.
- Assha: Ɓata Gari Sun Bankawa Motoci 10 Wuta A Filato
- Batun Musanya Sunan Titin Murtala Da Na Soyinka, Ba Gaskiya Ba ne – Minista
Draktan huldda jama’a da yada labarai na rundunar, Edward Gabkwet, ya ce an kai harin ne a wata maboyar ‘yan bindiga da ke kauyen Gidan Kare a karamar hukumar Faskari a jihar.
Sojojin sun kai harin ne ranar Asabar a lokacin da suka samu rahoton cewa ‘yan bindiga kimanin 100 sun kai hari wani kauye da ke da nisan kilomita biyar daga Gidan Kare, inda suka rika kone gidaje da dama.
Ta kara da cewa da misalin karfe 9:40 na daren ranar ne jirgin rundunar ya yi ruwan wuta a kan ‘yan fashin dajin wadanda suka taru a kusa da dabar Kuka Shidda, inda bayanai suka tabbatar da cewa an kashe sama da 80 daga cikinsu tare da kone babura 45.
A baya-bayan nan dai rundunar sojin saman Nigeriya na ci gaba da kai hare-hare a yaƙi da ta yi da ‘yan bindiga, musamman a yankin Arewa Maso Yamma.