Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa (NOA) ta bayyana cewa, hukumomin tsaro sun gudanar da manyan ayyuka a fadin kasar a cikin watan Agusta, wanda ya yi sanadin kame daruruwan mutane, da kwato miyagun kwayoyi, tare da ƙwato kadarori.
Darakta-Janar na NOA, Lanre Issa-Onilu, ya bayyana hakan a taron manema labarai na wata-wata da aka yi a Abuja ranar Litinin, yana mai bayyana cewa, an samu nasarar ne biyo bayan hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da na leken asiri.”
- An Kama Mutane 30 Da Zargin Laifin Aikin Dabanci A Yayin Zagayen Maulidi A Neja
- Xi Zai Halarci Taron Kolin Shugabannin Kasashen BRICS Ta Kafar Bidiyo
A cewarsa, sojojin Nijeriya sun aiwatar da hare-hare 261 a fadin kasar, tare da dakile hare-hare, da tarwatsa gungun ‘yan tada kayar baya, da kuma kubutar da fararen hula da aka sace.
Ya ce: “A Zamfara an kashe ‘yan ta’adda 30 a hare-haren sama da kasa, yayin da masu tada kayar baya 76 da suka hada da mata da kananan yara suka mika wuya ga jami’an tsaro.
“Rundunar ‘yansanda ta bayar da rahoton kama mutane 1,950 da ke da alaka da munanan laifuka, garkuwa da mutane, da kuma fashi. An kubutar da jimillar mutane 141 da aka yi garkuwa da su.
Ya ce hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta kama sama da kilo 66,000 na miyagun ƙwayoyi.
A ɓangaren Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annuti (EFCC), ya ce hukumar ta yi nasarar gurfanar da ƙorafe-ƙorafe 588 ga kotu a cikin watan Agusta kaɗai, inda ta ƙwato sama da naira biliyan 21 daga wasu kadarori na cin hanci da rashawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp