Dakarun Sojin Operation Hadin Kai tare da taimakon Civilian Joint Task Force (CJTF), sun kama wani da ake zargi da yi wa ‘yan Boko Haram safarar man fetur a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
An kama wanda ake zargin, mai suna Ahmadu Mohammed Dogo, a unguwar Muna Garage da misalin ƙarfe 11:50 na safiyae ranar Litinin, bayan samun sahihin bayani.
- Kwamishinan Sufuri Ya Yi Murabus Kan Belin Wani Da Ake Zargi Da Laifin Safarar Kwaya A Kano
- Hare-haren Boko Haram Da ‘Yan Bindiga Ya Ragu A Cikin Shekaru Biyu – Ribadu
Rahotanni sun bayyana cewa yana ƙoƙarin boye man fetur a cikin kwalaben lemo, wanda aka lulluɓe a cikin buhun guda 12.
Ya amsa cewa yana shirin kai man ne zuwa garin Gamboru-Ngala, kusa da iyakar ƙasa, wadda ta ke hanyar da ‘yan ta’adda ke bi don samun kayan aiki.
Sojoji sun kuma gano abubuwa irin su: man da aka cika a kwalabe, miyagun ƙwayoyi, zobba, allurai, da wasu kayayyakin da ake yin sihiri da su.
Hukumomi sun ce wannan kame na daga cikin ƙoƙarin hana Boko Haram samun kayan aiki da kuɗaɗe a yankin Arewa maso Gabas.
Yanzu haka an killace wanda ake zargin, kuma ana ci gaba da bincike a kansa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp