Hedikwatar tsaro (DHQ) ta bayyana cewa, sojojinta sun kama mutane 107 da ake zargi da aikata ta’addanci, garkuwa da mutane, satar danyen mai da sauran wadanda ake zargi da aikata laifuka a fadin kasar nan.
Darakta mai kula da harkokin yada labarai na tsaro, Maj.-Gen. Markus Kangye wanda ya bayyana hakan a ranar alhamis ya kuma ce sojojin sun kuma kubutar da mutane 20 da aka yi garkuwa da su.
- ‘Yansanda Sun Kama Wani Mai Garkuwa Da Mutane, Sun Ceto Wani Yaro Ɗan shekara 2 A Yobe
- Gwamna Lawal Ya Ziyarci Yankunan Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Wa Hari A Zamfara
Maj.-Gen. Kangye ya bayyana haka ne yayin da yake ba da bayanai kan ayyukan soji a tsakanin ranakun 7 zuwa 14 ga watan Agusta, 2025.
A yankin Arewa-maso-Gabas, ya ce sojojin, sun kawar da ‘yan ta’adda da dama, sun lalata sansanonin kayan aikinsu, sun kwato makamai, sun wargaza hanyoyin hada-hadarsu tare da samar da amintaccen wuri don sake tsugunar da ‘yan gudun hijira.
A cewar Kangye, sojojin sun kama mutane 37 da ake zargin ‘yan ta’adda ne, tare da kubutar da mutane biyar da aka yi garkuwa da su, tare da kwato makamai, alburusai, kayayyakin masarufi, motoci da babura, sannan kuma sun warware wasu bama-bamai cikin nasara a yankin.
Da yake ba da rahoto kan yankin Arewa maso Yamma, Kangye ya ce sojoji sun kama mutane 11 da ake zargin ‘yan ta’adda ne tare da kubutar da mutane 17 da aka yi garkuwa da su a wasu hare-hare.
Hakazalika a yankin Arewa ta tsakiya, daraktan ya bayyana cewa sojoji sun kama mutane 15 da ake zargi tare da ceto mutane tara tare da kwato wasu kayayyaki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp