Dakarun Runduna ta 6 na Sojojin Nijeriya sun kama mutane 50 da ake zargi da hannu a fasa-kwaurin danyen mai da kuma tace shi ba bisa ka’ida ba a wasu sassan yankin Neja-Delta.
An gudanar da wannan samame tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro tsakanin ranakun 30 ga Yuni zuwa 13 ga Yuli, 2025, inda aaka yi nasarar rushe haramtattun wuraren tace mai guda 11 da kwace lita 25,000 na ɗanyen mai da aka sace.
- Yadda Tinubu Ya Karrama Sojojin Da Aka Kashe A Neja Delta
- Majalisar Dattawa Ta Fara Binciken Satar Mai A Yankin Neja-Delta
Kakakin rundunar, Lt.-Col. Danjuma Jonah Danjuma, ya bayyana cewa an gano wuraren da aka haɗa bututun mai ba bisa ka’ida ba, sannan dakarun sun ci gaba da daƙile ƙoƙarin masu satar mai ta hanyar kafa sabbin sansanonin fasa-kwauri a yankin.
A Jihar Ribas, an rushe sansanonin fasa-kwauri, an lalata injuna da dama, an kuma ƙwato lita 6,000 na ɗanyen mai a yankin Imo River, tare da lalata wasu kayayyaki da dama.
A wasu wurare kamar Obuzor da Ozaa West a Abia da Ribas, an kwato ɗanyen mai da sauran kayayyaki, haka-zalika a Obiafor an rushe sansanin fasa-kwauri tare da kwato lita 3,000 na man dizal da lita 2,000 na man fetur, da lita 1,000 na ɗanyen mai. A Okarki Forest, an lalata wuraren ajiya da dama, yayin da a Delta, aka kama kwale-kwale dauke da lita 1,720 na ɗanyen mai da aka sace.
A Bayelsa, an kwace kayan aikin da aka tanada don fasa bututun mai, tare da kama wasu da ake zargi. A Akwa Ibom kuma, an gano jarkoki 15 cike da man dizal da aka tace ba bisa ƙa’ida ba. Rundunar ta ce za ta ci gaba da mamaye yankuna da kuma hana masu laifi damar gudanar da ayyukansu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp