Sojojin runduna ta 6 sun kashe ‘yan fashin daji 2 tare da kwato shanu 1,000 a ƙauyen Jebjeb na ƙaramar hukumar Karim-Lamido, jihar Taraba.
Mai magana da yawun Brigade na 6, Kyaftin Olubodunde Oni, ya bayyana cewa sojojin sun mayar da martani ne bayan samun rahoton cewa wasu ‘yan fashi dauke da makamai kan babur 30 sun shiga jihar daga Plateau domin yin fashi.
“Masu laifin sun kai hari wani gari na Fulani da ke kusa da Jebjeb domin sace shanu. Sojojin sun bi su har zuwa dajin Madam na Plateau inda aka yi musayar wuta,” in ji Oni.
Ya ƙara da cewa Sojojin sun kashe ‘yan fashi 2 kuma sun ƙwato shanu kusan 1,000, waɗanda aka mayar da su cikin aminci zuwa ƙauyen Jebjeb.
An kuma bayyana cewa za a gudanar da bincike don tabbatar da an mayar da shanun ga masu su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp