Sojojin Nijeriya na rundunar Operation Haɗin Kai a Arewa maso Gabas sun kashe ‘yan ta’adda 14 a cikin hare-hare daban-daban da suka kai tsakanin ranakun 21 zuwa 27 ga watan Satumba a jihohin Borno da Adamawa. Rundunar ta kuma kwato manyan makamai, da alburusai, da kwayoyi da takin zamani da ake amfani da shi wajen haɗa bama-bamai.
A ranar 27 ga watan Satumba, Sojoji sun fatattaki mayaƙan Boko Haram a ƙaramar hukumar Mafa, inda suka kashe 11 daga cikinsu tare da kwace bindigogin AK-47 guda hudu. A Adamawa kuma, dakarun sun samu nasarar kwace bindiga a ƙaramar hukumar Hong, sai kuma a Magumeri, Borno, inda aka samu wata bindiga daga hannun masu garkuwa da mutane.
- Nazari Kan Littafin Baba Zube Na 5 (Gwamnati)
- An Yanke Wa Sojojin Da Suka Sayar Wa ‘Yan Ta’adda Makamai Hukuncin Ɗaurin Rai-da-rai A Borno
A wani hari da ‘yan ta’adda suka kai a sansanin Soji da ke Damboa a ranar 25 ga watan Satumba, Sojojin sun daƙile farmakin tare da kashe wasu daga cikin maharan.
Haka zalika, dakarun sun gano takin zamani mai yawa a garin Mubi, jihar Adamawa, da kuma jarkokin man fetur guda 20 da ake zargin ‘yan ta’adda na amfani da su. Rundunar Sojin ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da kai hare-hare domin karya ƙarfin masu tayar da ƙayar baya a yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp