A ci gaba da yaki da ta’addanci da dakarun sojin Nijeriya ke yi, sun sake kashe wasu mayakan Boko Haram a yankin Bama da ke Jihar Borno.
Dakarun runduna ta 21 na Operation Hadin Kai sun samu nasarar ne a ranar Talata 14 ga watan Mayu, 2024.
- Hukumar NSCDC Ta Kama Wasu Mutane 9 Da Ake Zargi Da Aikata Fashi A Kano
- Biyan Tukuici: Gwamna Yusuf Ya Ƙaddamar Da Tallafin Naira 50,000 Ga Mata 5,200 Duk Wata A Kano
Dakarun sojin sun yi wa ‘yan Boko Haram din barin wuta a Garin Fallujah da ke yankin karamar hukumar Bama a jihar.
Dakarun sojin sun tabbatar da aniyarsu na ci gaba da kai hare-hare domin tabbatar da zaman lafiya a jihar da ma wasu sassan Nijeriya.
Boko Haram dai ta shafe shekaru tana kai hare-haren ta’addanci, wanda ya yi sanadin mutuwar dubban mutane, tare da raba wasu da muhallansu.