Dakarun runduna ta hudu ta Operation Whirl Punch, da runduna ta musamman ta bataliya ta 167, sun kubutar da mutane 14 da aka yi garkuwa da su yayin da suka farwa wata maboyar ‘yan fashi da makami a jihar Kaduna.
Kwamishinan ma’aikatar harkokin tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ya ce, sojojin da sun sintiri mai zuwa yankin Tukurua a karamar hukumar Chikun ta jihar, sun yi artabu tare da fatattakar ‘yan ta’addan da kashe daya daga cikinsu.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 2 Tare Da Yin Garkuwa Da Matan Aure 4 A Kaduna
- Sojoji Sun Ceto Mutane 6 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kaduna
Sanarwar ta bayyana cewa, sojojin sun ceto mutane 14 da aka yi garkuwa da su, wadanda suka hada da maza tara da mata biyar.
Aruwan ya ci gaba da cewa, gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana jin dadinsa dangane da rahoton tsaron, ya yabawa rundunar tare da yaba wa jagorancin Manjo Janar TA Lagbaja da kuma kwamandan runduna ta Operation Whirl Punch.
Gwamnan ya kara yabawa kwazon sojojin, domin an kubutar da dukkan wadanda aka yi garkuwa da su a raye ba tare da wani rauni ba.