Dakarun sojin Nijeriya tare da haɗin gwiwar Operation Whirl Stroke da Operation Safe Haven sun kashe ‘yan bindiga biyu tare da ƙwato shanu 1,000 da aka sace a ƙauyen Jebjeb da ke ƙaramar hukumar Karim-Lamido a Jihar Taraba.
Mai magana da yawun rundunar, Kyaftin Olubodunde Oni, ya ce sojojin sun samu sahihin bayanai kan wani hari da ‘yan bindiga kusan 30 a kan babura suka kai, inda suka shiga Taraba daga Jihar Filato domin aikata laifi.
- Xi Jinping Ya Jaddada Wajibcin Koyi Da Nagartattun Halayen Wasu Mutane Masu Bukata Ta Musamman
- Nijeriya Na Bukatar Dala Biliyan 10 Kowace Shekara Domin Samun Ingantacciyar Wutar Lantarki — Minista
‘Yan bindigar sun kai wa wasu Fulani da ke ƙauyen Jebjeb hari, inda suka sace shanu.
Sojoji daga Taraba da Filato sun haɗa kai suka nufi ƙauyen Komodoro domin tare su.
Oni, ya ce ‘yan bindigar sun yi ƙoƙarin tserewa zuwa Dajin Madam da ke Jihar Filato, amma sojoji suka bi su.
A lokacin musayar wuta, sojojin sun harbe biyu daga cikin ‘yan bindigar kuma suka ƙwato shanun da suka sace.
An dawo da shanun zuwa ƙauyen Jebjeb, kuma rundunar sojojin ta ce za tantance su domin mayar da shanun ga masu su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp