Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa dakarun Operation Forest Sanity sun kubutar da wasu mutane 16 daga hannun masu garkuwa a wani samame da suka kai kan hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna da wani wuri a karamar hukumar Igabi a jihar.
Kwamishinan ma’aikatar tsaron cikin gida da harkokin cikin gida Samuel Aruwan, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce, bisa ga bayanan da jami’an tsaro suka bayar, sojojin sun dakile harin ne a kan hanyar Udawa-Manini ta hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna.
Aruwan ya ce, sojojin na Operation Forest Sanity sun kuma sami wani rahoton sirri na isowar gungun ‘yan bindigar daga kauyen Gonar Dakto da ke karamar hukumar Igabi, inda suka yi musu kwanton bauna a madatsar hanyar kauyen Maraban Huda.
“An ceto wani da aka yi garkuwa da shi duk da cewa ‘yan bindigar sun yi masa rauni da yawa amma an garzaya da shi Asibitin Jaji Cantonment domin yi masa magani” inji shi.
Ya kara da cewa, “Bugu da kari kuma a wani bayanan sirri na ‘yan ta’adda da aka samu, sojojin Operation Forest Sanity sun kai harin kwanton bauna a kusa da babban yankin Mangoro da ke karamar hukumar Chikun-Birnin Gwari da ke kan iyaka da karamar hukumar Shiroro ta Jihar Neja.
“Sojojin sun kashe biyu, sun kuma kwato bindiga kirar AK47 guda daya da bindigar famfo ta gida guda daya da bam guda daya da kuma babura 10.”