Dakarun rundunar sojin Nijeriya ta daya da ke aiki a yankin Kaduna, sun halaka ‘yan bindiga bakwai a kauyen Udawa da ke karamar hukumar Chikun a jihar.
Wannan na cikin wata sanarwa da mukaddashin daraktan hulda da jama’a na rundunar sojin, Laftanar Kanar Musa Yahaya ya fitar.
- ‘Yansanda Sun Ceto Wadanda Aka Yi Garkuwa Da Su A Abuja
- Ƴansanda Sun Kashe Ƴan Bindiga 2 Sun Ƙwato Bindigu 2 da Alburusai
A cewarsa sojojin da aka tura zuwa Udawa sun gudanar da sintiri a kan hanyar Udawa zuwa kurebe a ranar Lahadi, kuma yayin wata arangama da ‘yan bindiga, sun samu nasara a kan su suka lalata wasu daga cikin kayayyakinsu.
A yayin samamen dakarun sun kwato makamai da dama daga hannun maharan da suka hada da bindiga kirar AK-47 da babu komai a ciki da bindiga ta daban da harsashi shida da wasu abubuwa masu hatsari.
Kazalika, sojojin a wani samame da suka kai a kauyen Kwaga da ke karamar hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna, sun yi nasarar kashe biyu daga cikin ‘yan bindiga tare da kwato bindigogin AK-47 guda biyu, da harsasai da babura biyu.
A wani samame da aka kai a garin Sabo Birni da ke karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna, sojojin sun kama wasu da ake zargin ’yan bindiga ne a kauyen Baka yayin wata arangama, inda wasu daga cikinsu suka tsere da raunuka da dama sanadiyyar harbin bindiga.
Dakarun da ke aikin sun yi amfani da yankin gaba daya tare da kwato bindiga kirar AK-47 guda daya da babura biyu.