Hedikwatar tsaro ta bayyana cewa, Rundunar sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 185, tare da cafke 212 da ake zargi da aikata laifuka, ta kuma kubutar da mutane 71 da aka yi garkuwa da su a fadin Nijeriya cikin mako guda.
Daraktan ayyukan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba, wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Juma’a, ya ce munanan ayyukan masu garkuwa da mutane da yawaitar hare-harensu ya dusashe hasken nasarorin da sojojin ke samu wajen yakar ‘yan ta’addan a fadin kasar nan.
- Rashin Tsaro A Nijeriya: Gazawar Masu Mulki Ce Da Cin Amanar Kasa
- Muna Bin ‘Yan Bindiga Har Maboyarsu Mu Fatattake Su – Minista
Sai dai ya ce, sojojin sun kama mutane 44 da ake zargin barayin mai ne tare da kwato lita 815,980 ta danyen mai da aka sace, lita 163,675 ta AGO da aka tace ba bisa ka’ida ba, da kuma lita 1,750 na kananzir da kudinsu ya kai N1,065,885,050.00.
Daraktan ya ce sojojin sun kwato makamai iri-iri 224 da alburusai iri-iri 2,337.
Har ila yau, sojojin sun gano tare da lalata haramtattun wuraren tace danyen mai guda 51, kwale-kwale 61, tankunan ajiya 56, motoci 13, tukwanen girki 78 da injinan ban ruwa guda hudu.