Dakarun sojojin Nijeriya sun kama wasu manyan ‘yan ta’adda guda hudu tare da kwato makamai a jihar Borno.
Rundunar sojin Nijeriya a cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X, ta ce, sojojin a ranar 29 ga Satumba, 2024, sun kai farmaki kan maboyar mayakan Boko Haram/ISWAP a kauyukan Ajiri da Mastari na karamar hukumar Bama ta jihar.
- Zamfara Ta Yi Bikin Cika Shekaru 28 Da Kafuwa Tare Da Murnar Samun ‘Yancin Nijeriya
- Zaɓen Ƙananan Hukumomi: Gwamna Uba Sani Ya Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC
A cewar sanarwar, an kashe wasu fitattun ‘yan ta’adda guda hudu a yayin da sojojin suka kwato bindigar harba roket guda biyu, mujallun AK-47 guda biyu, harsashi 28 masu nauyin 7.62mm da sauran makamai.
A wata arangama, sojoji a mahadar Banki da ke karamar hukumar Bama sun sake harbe wani dan ta’adda.