Hukumar Tsaro Ta Kasa (DHQ) ta ce, dakarun soji a farmakin da suka kaddamar kan ‘yan ta’adda a sassan kasar nan, sun kashe ‘yan ta’adda 59, sun ceto wadanda aka yi garkuwa da su 88, sun kwato makamai 68 da kuma alburusai 1,364.
Daraktan sashen yada labarai na hukumar tsaron, Manjo Janar Edward Buba, wanda ya shaida hakan ta cikin sanarwar da ya fitar a ranar Juma’a, ya ce, sojojin sun kuma cafke ‘yan ta’adda 88, masu garkuwa da mutane 10 da kuma ‘yan fashin daji 20.
Ya ce: “Zuwa ranar 28 ga watan Yulin 2023, sojoji sun hallaka ‘yan ta’adda 59, an kama ‘yan ta’adda 88, masu garkuwa da mutane 10, da ‘yan bindiga 20 hade da wasu mutum 19 da ake zargin barayin Mai ne. Kazalika, sojojin sun ceto mutum 88 da aka yi garkuwa da su.”
Ya jero muggan makaman da suka kwato da suka hada da bindiga kirar AK47 guda 26, GPMG guda daya, bindiga kirar AKMS, bindiga kirar FN, bindigar gida guda hudu, fistol biyar, wasu bindigar kirar gida guda 19.
Alburusai kuwa da suka kwato sun hada da 1,083 samfurin 7.62mm special, 228 7.62mm NATO, 14 5.56 x 45mm, jakar alburusan AK47 guda 15 a shake, 9mm ammo guda 9, da tsabar kudi naira N41,915.00 da kuma kudin CFA 49,000.
Sauran sun hada da danyen litar mai 323,650 da aka sata, lita 128,700 na AGO da litar DPK guda 4,000 liters of DPK, sannan danyen mai da aka sata da aka kiyasce zai kai na N388,441,660.00 aka kwato.