Dakarun sojojin Nijeriya na Operation Hadin Kai tare da hadin gwiwar ‘yan banga a daren ranar Litinin sun kashe ‘yan ta’addan Boko Haram takwas tare da kama daya da ransa a wani harin kwantan bauna da suka kai a karamar hukumar Mafa ta jihar Borno.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, an samu nasarar ne bayan babban hafsan sojin kasa (COAS), Laftanar Janar Farouk Yahaya, ya bukaci sojoji da su ninka kokarinsu wajen fatattakar ‘yan ta’adda a dajin Sambisa da yankin tafkin Chadi.
An tattaro cewa, harin kwantan baunan da aka samu nasara, an samu nasarar ne yayin da sojojin suka fatattaki ‘yan ta’addan nan take.
A cewar wani rahoto da aka samu daga majiyoyin leken asiri na Zagazola Makama, wani mai sharhi kan harkokin tsaro kuma masani kan yaki da tada kayar baya a tafkin Chadi, yace, ‘yan ta’addan sun kasance wadanda suka saba yin fashi da makami a babban yankin karamar hukumar Mafa da Jere da Konduga.