Akalla ‘yan ta’adda 150 ne sojojin Nijeriya suka kashe a wasu hare-hare daban-daban a Arewacin kasar nan.
Daraktan yada labarai na rundunar, Manjo-Janar Musa Danmadami ne ya bayyana hakan yayin taron tattaunawa na mako biyu a hedikwatar tsaro da ke Abuja.
- ‘Yansanda Sun Cafke Mutum 9 Da Ake Zargi Da Kai Wa Tawagar Atiku Hari A Borno
- 2023: Na Shirya Tsaf Don Fara Fita Yakin Neman Zabar Tinubu Da Sauran ‘Yan Takarar APC –Buhari
Ya ce an kama kimanin ‘yan ta’adda 100 da suka hada da masu samar da kayan aiki, masu hada baki da kuma ‘yan leken asirin Boko Haram.
A cewar Manjo-Janar Danmadami daga ranar 1 ga watan Disamba, 2022 zuwa yau, sama da ‘yan Boko Haram da ISWAP 423 suka mika wuya ga sojoji, yayin da aka kubutar da dimbin fararen hula da aka sace daga sansanonin ‘yan ta’addan.
Da yake karin haske kan ce-ce-ku-cen da ake yi dangane da harin da sojojin saman Nijeriya suka kai kauyen Malale-Mutumji da ke Jihar Zamfara, inda aka ce an kashe wasu fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba, kakakin rundunar tsaron ya ce an fara gudanar da bincike kan lamarin domin gano ko an samu asarar rayuka.
Ya ce, duk da haka, ya tabbatar da cewa an yi harin ne da nufin kawar da abubuwan da ‘yan ta’adda.
A cewarsa, sojoji ba za su taba kai wani hari ta sama da zai kai ga rasa rayukan wadanda ba su ji ba ba su gani ba.
“A gaskiya, lokacin da dama idan muka fahimci cewa kai hari kan masu aikata laifuka zai haifar da asarar rayuka fararen hula, mu kan dakatar da irin wannan hari,” in ji shi.