Dakarun Sojojin Nijeriya sun yi ruwan bama-bamai a sansanin ‘yan ta’addar Daesh a yankin Yammacin Afirka (ISWAP), inda suka kashe ‘yan ta’adda da dama a jihar Yobe.
LEADERSHIP ta rawaito cewa, ‘yan ta’addar sun hadu ne akan babura sun nufi wurin da niyyar kai hari a sansanin Soji.
- ISWAP Ta Sace Jami’an Tsaro 7 A Borno
- Da Dumi-dumi: Mayakan ISWAP Sun Kai Wa ‘Yan Boko Haram Farmaki
Wani rahoton sirri da Zagazola Makama, kwararre a fannin yaki da tada kayar baya a yankin tafkin Chadi ya samu daga manyan majiyoyin soji, wanda ya samu wakilinmu, ya nuna cewa, a bisa bayanan sirri, sojojin bataliya ta 27 Task Force Battalion, sun harba makaman atilare da dama. ‘yan ta’addar da suka yi sanadiyar kashe mutanen da ba a tantance adadinsu ba.
An kuma bayyana cewa daga baya ‘yan ta’addar sun dawo a kan babura 6 da mota daya domin kwashe gawarwakinsu.
A wani labarin kuma, wani jami’in ‘Civilian Joint Task Force’ (CJTF) ya rasa ransa yayin da wasu 4 suka jikkata a wani samame da ‘yan ta’addan ISWAP suka kai da tsakar dare a kauyen Benisheik da ke karamar hukumar Kaga a jihar Borno.
Benisheikh yana da nisan kilomita 72 da nisan mil 44.8 zuwa Maiduguri babban birnin jihar Borno.
An rawaito cewa ‘yan ta’addan sun kutsa cikin garin ne a kan babura da misalin karfe 3:30 na safe inda suka yi artabu da jami’an tsaro.
Wani rahoton leken asirin da Zagazola Makama ya samu ya ce ‘yan ta’addar sun yi galaba a kan jami’an tsaro, inda suka kashe daya daga cikinsu da kona motocin sintiri hudu.
Majiyar ta bayyana cewa ‘yan ta’addar sun ja da baya inda suka yi taho-mu-gama a lokacin da suka hango wata tawaga ta hadin gwiwa da sojojin Nijeriya.
Idan dai za a iya tunawa, Makama ya yi gargadin cewa ‘yan ta’addar na shirin kai hare-hare da dama a wasu wurare a fadin kasar nan tsakanin Satumba da Oktoba, 2022.