Sojoji a jihar Katsina sun ceto mutane 35 da masu garkuwa da mutane yi awon gaba da su a makon da ya gabata a kauyukan Tashar Nagulle da Nahuta a karamar hukumar Batsari.
Maharan tun da farko sun bukaci a biya su kudin fansa har naira miliyan 60 domin su saki wadanda suka sace.
- ‘Yansanda Sun Dakile Harin ‘Yan Ta’adda, Sun Ceto Mutum 3 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina
- Ma’aikatan Kiwon Lafiya 83 Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina Cikin Shekara 8 – MHWUN
Kubutar da wadanda harin ya rutsa da su da Sojojin Nijeriya suka yi ya sanya farin ciki da annashuwa a yankin da abun ya faru.
Shugaban karamar hukumar Batsari, Yusuf Mamman-Ifo, ya bayyana farin cikinsa da wannan ci gaba, musamman ganin duk wadanda abin ya shafa an same su cikin koshin lafiya da walwala.
“Nasarar kubutar da mutanen ta biyo bayan addu’o’i da goyon bayan da gwamnan jihar ke ba mu da jami’an tsaro a kodayaushe, yana karfafa mana guiwa.
“Karnel din da ya jagoranci aikin ya yi aiki mai kyau. Za mu ci gaba da baiwa jami’an tsaro bayanan sirri,” cewarsa.
Daya daga cikin wadanda aka ceto daga hannun ‘yan bindigar, Maryam Nagulle, ta bayyana yadda lamarin ya faru, inda ta bayyana cewa an yi awon gaba da su tare da saka su tattaki na tsawon sa’o’i bakwai da rabi zuwa sansanin ‘yan ta’addar da ke dajin da aka kai su.
“Muna kulle a dakin muka ji karar harbe-harbe, sai ‘yan ta’addar suka gudu, sojoji suka ci gaba da harbi, ba muka yi gum da bakinmu cikin dakin, sai sojoji suka zo suka zo suka ceto mu. ” A cewarta.