Hedikwatar tsaro, (DHQ) ta ce dakarun hadin guiwa na Operations DELTA SAFE sun gano tare da lalata wuraren tace haramtacciyar matatar mai 30 tare da kama masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa su 42 a cikin makwanni uku.
Wannan na kunshe ne a cikin wata takarda da sashen yada labarai na dakarun tsaron ya fitar ta bakin, Birgediya Janar Abdullahi Ibrahim, kan ayyukan da sojoji suka yi a tsakanin 15 ga Yuni zuwa 6 ga Yuli 2023.
- ‘Yansanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Mutum 12 Yayin Tashin Bam A Wurin Hako Danyen Mai A Ribas
- Matatar Man Dangote Za Ta Samar Da Karin Hasken Wutar Lantarki A Nijeriya – Gwamnan CBN
Ya ce sojojin a kokarinsu na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a bangaren kula da harkokin kasuwanci a shiyyar Kudu maso Kudu na Nijeriya, sun gudanar da wani samame, kan yaki da haramtattun matatun man fetur a garuruwan Delta, Bayelsa, Ribas da Jihar Cross River.
Ya ce an gudanar da samamen ne da nufin dakile masu aikata laifuka ‘yancin ci gaba da aika-aikar da suke.
Sakamakon haka, sojojin sun gano tare da lalata haramtattun matatun man fetur a wuraren hanya guda 30 da tankunan ajiyar mai 125, da jiragen ruwa na katako guda 21 da wasu ababe da dama.
Sojojin sun kuma kwato litar danyen mai lita 1,675,700 da lita 74,500 na Man Fetur da Motoci 10 sai Babura 20 da Makamai 8 da alburusai iri-iri har 330 da cafke masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa su 42.
Ya ce, tuni an mika duk wasu kayayyakin da aka kwato daga hannun masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa da aka kama, an kuma mika su ga hukumar da ta dace domin daukar mataki.