Dakarun rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa (MNJTF), a ranar Litinin din da ta gabata, sun dakile wani hari da suka kai musu a garin Arege da ke Arewa maso Gabashin jihar Borno, ba tare da an samu asarar rayuka ba.
Sojojin sun fatattaki ‘yan ta’addar ISWAP a cikin nasarar da suka samu na kafa sojoji a ranar 30 ga Mayu, 2022.
- ‘Yan Ta’adda Sun Yi Awon-Gaba Da Matafiya Da Yawa, Sun Kona Motoci 8 A Kaduna
- Fada Ya Barke Tsakanin Shugabannin ’Yan Bindiga, 2 Sun Mutu Yayin Rikicin A Zamfara
Sojojin sun ce ‘yan ta’addan sun kai hari garin ne a daren ranar Litinin, 30 ga watan Mayu, 2022, ta bangarori da dama tare da wasu da ba a tabbatar da adadinsu na ISWAP ba.
Zagazola Makama, kwararren masani a fannin yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, ya bayyana cewa wasu ‘yan ta’adda da dama sun tsere da raunukan harbin bindiga.
Kazalika wasu majiyoyin sun tabbatar da cewa ba a samu asarar rai ba a bangaren sojoji yayin samamen.
Kayayyakin da aka kwato daga hannun ‘yan ta’addan sun hada da; Hilux daya, bindigar Anti Air Craft da harsashi da yawa da kuma mujallu AK47 guda uku.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp