Runduna ta 7 ta sojojin Nijeriya da ke Maiduguri, ta tabbatar da kama wani soja bisa zargin Harbe wani direban babbar mota har lahira a wani shingen binciken ababen hawa da ke kan hanyar Maiduguri zuwa Dikwa- Gamboru.
Lamarin ya faru ne biyo bayan rashin fahimtar juna da aka samu tsakanin sojan da direban babbar motar a shingen binciken ababen hawan.
- Ta Shiga Caji Ofis Ta Harbe Saurayinta Dan Sanda Har Lahira
- INEC Ta Tilasta Wa Daraktocinta 4 Yin Ritaya
Lamarin wanda ya faru a ranar jajibarin Kirsimeti, ya janyo tsaikon zirga-zirgar ababen hawa akan titin sakamakon zanga-zangar da direbobin motocin suka yi.
Da yake tabbatar da cafke sojan da ya aikata wannan laifi a ranar Alhamis a wata sanarwa, jami’in hulda da jama’a na runduna ta 7, Laftanal Kanal A.Y. Jingina, ya ce, rundunar ta fara gudanar da bincike bayan sun samu korafi daga kungiyar ma’aikatan sufuri ta kasa (NURTW).
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp