Rundunar soji ta cafke mutum guda tare da kwato wasu muggan makamai da alburusai bayan tarwatsa wata masana’antar kera makamai a gundumar Heipang da ke karamar hukumar Barkin Ladi a jihar Filato.
Da yake bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, kakakin rundunar haɗin gwiwa ta rundunar ‘Operation Enduring Peace’, Manjo Samson Zhakom, ya ce, an kai samamen ne biyo bayan samun bayanan sirri a ranar 17 ga Satumba, 2025.
A cewarsa, sojoji sun kai samame cikin masana’antar, inda suka kama wani mai ƙera makami, yayin da wasu kuma suka tsere.
Zhakom ya ƙara da cewa, wanda aka cafken da kuma kayayyakin da aka ƙwato suna hannun rundunar domin ci gaba da bincike, kuma rundunar za ta ci gaba da farmakar wadanda suka tsere daga haramtacciyar masana’antar kera makaman.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp