Dakarun Operation Safe Haven (OPSH) da ke aiki da rundunar soji ta musamman da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Filato da wasu sassan jihohin Bauchi da Kaduna, sun ki amincewa da karbar cin hancin Naira miliyan 1.5 daga wasu da ake zargin barayin shanu ne a Filato.
Jami’in yada labarai na rundunar Kyaftin James Oya ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai ranar Laraba a birnin Jos.
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 7 Da Cafke 33 A Kaduna Da Filato
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 6 Tare Da Kama Wasu A Filato
Oya ya ce sojojin da ke aiki a rukuninsu na hudu sun kama wasu da ake zargin barayin ne da suka ba su cin hanci.
Ya bayyana cewa ma’aikatan takwas da suka ki karbar cin hancin sun cancanci a yaba musu da kwamandan rundunar ta su Manjo-Janar. Abdusalam Abubakar.
“OPSH ta karrama jami’anta takwas bisa kin karbar cin hancin Naira miliyan 1.5 daga wasu da ake zargin barayin shanu ne a Filato.
“Ma’aikata takwas da aka tura a sashin OPSH na hudu, sun kama barayin shanu 30 a wani shingen bincike da ke kusa da Bisichi a karamar hukumar Barkin Ladi a jihar.
“An yi awon gaba da shanun na wani mai suna Shehu Umar a garin Mangu inda aka kai su wani wuri da ba a san ko ina ba, yayin da dakarun nasu suka kama su a lokacin da suke aikin bincike.
“Wadanda ake zargin, Anas Usman mai shekaru 20 da Gyang Cholly mai shekaru 42, nan take suka tunkari rundunar da nufin ba su cin hanci da kuma tabbatar da tsaron shanun da aka sace.
“An ki amincewa da neman bukatar a karbi kudin da aka kama wadanda ake zargin suka bayar na cin hanci,” cewarsa.
Oya ya ce kwamandan wanda ya yaba wa sojojin bisa jarumtaka da kuma yin abin koyi, ya bukaci sauran jami’an tsaro da su yi koyi da wannan gagarumin yunkuri na kare rayuka da dukiyoyin jama’a a jihar.