A shekarar 2022 da muke ciki, rundunar sojojin kasar Sin sun aiwatar da ra’ayin gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adam, da dagewa wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyan rundunar sojan babbar kasa, da aiwatar da hadin gwiwar soja ta kasa da kasa yadda ya kamata, tare da samun sakamako mai inganci.
Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron kasar Sin Tan Kefei, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka saba yi jiya Alhamis cewa, a shekarar 2022, ayyukan hadin gwiwar sojojin kasa da kasa da rundunar sojan kasar Sin ta yi, sun ba da kyakkyawar gudummawa wajen kiyaye ikon mallakar kasa, tsaro, moriyar ci gaba, kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, da kuma ba da hidima wajen gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adam.
Kakakin ya bayyana cewa, tun daga farkon wannan shekarar, rundunar sojojin kasar Sin, ta shirya tare da halartar atisayen soja da wasanni da horaswa na hadin gwiwa da kasashen ketare, hakan ya zurfafa amincewa da juna da hadin kai tare da rundunonin sojojin kasashen da abin ya shafa, da taka muhimmiyar rawa wajen inganta matsayin horaswa tamkar na yaki.
Ya kara da cewa, rundunar sojojin kasar Sin za ta ci gaba da fadada da zurfafa huldar soji da kasashen ketare, da karfafa yin hakikanan mu’amala da hadin gwiwa, da ba da sabbin gudummawa wajen wanzar da zaman lafiya a duniya, da sa kaimi ga samun ci gaba tare. (Mai fassara: Bilkisu Xin)