Dakarun Jamhuriyar Nijar sun cafke kasurgumin dan bindigar da ya addabi jihohin Arewa Maso Yammacin Nijeiriya, Kachallah Mai Daji.
Kachallah Mai Daji ya shiga hannun dakarun Jamhuriyar Nijar ne yayin da ya ke yukurin satar dabbobi a tsakanin iyakar Nijeriya da Nijar.
- Dillalai Sun Yi Barazanar Daina Kai Tumatir Jihar Legas
- Za A Samu Kyautatuwar Hadin Gwiwar Dake Tsakanin Sin Da Faransa
Rahotanni sun ce kasurgumin ɗan bindigar ya fi aikata aika-aikar ne a yankin Ilela, inda ya ke yin ta’addanci a kauyukan Tozai, Sabon Garin Darna, Darna Tsolawo, Tudun Gudali, Basanta, Ɗan Kadu, Takalmawa, Gidan Hamma, Ambarura, Gidan Bulutu da sauran kauyukan da ke yankin.
Wani masanin tsaro, Zagazola Makama, wanda kwararre ne a fannin yaki da ta’addanci ya ce Kachallah Mai Daji ya shafe sama da shekaru 10 yana addabar mutane a Nijeriya kafin ya sauya sheka.
Ya kara da cewa ya kashe mutane da dama, ya kuma kone kauyuka da yawa tare da sace mutane da yawa, baya ga haraji da ya dinga karba a hannun mutane na tsawon shekaru 10.