Gwamnatin jihar Kaduna ta ce, sojojin Nijeriya sun dauki alhakin jefa bam a Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna wanda ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 30 a ranar Lahadi.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, an kashe mutane da dama a kauyen Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna bayan da wani jirgin soji ya jefa bam a yayin da ake gudanar da taron Mauludi.
- Ranar Nakasassu: Gwamna Uba Sani Ya Nanata Kudirin Shigar Da Su Harkokin Jihar Kaduna
- Yadda Matakin Raya Kauyuka Da Sin Ta Dauka Ke Taimakawa Kawar Da Talauci Da Ma Yayata Aladun Kasar
Tun da farko dai, rundunar sojin saman Nijeriya, NAF ta musanta alhakin kai harin.
A cewar sanarwar da Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na rundunar sojin saman Nijeriya, Commodore Edward Gabkwet ya fitar, “NAF ba ta kai wani hari a Kaduna cikin sa’o’i 24 da suka gabata ba.”
Sai dai, kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida Samuel Aruwan, ya ce babban hafsan rundunar soji ta 1 ta Nijeriya da kwamandan rundunar Operation Whirl Punch, Manjo Janar VU Okoro, sun amince cewa, lamarin ya faru ne cikin kuskure yayin da rundunar sojojin Nijeriya ke ci gaba da yaki da ‘yan ta’adda a yayin gudanar da ayyukan rundunar na kullum.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai kula da harkokin tsaron cikin gida ya raba wa manema labarai jim kadan bayan da mataimakiyar gwamnan, Dakta Hadiza Balarabe ta gana da malaman addinin musulunci, da sarakunan gargajiya, da shugabannin hukumomin tsaro.
An gudanar da taron ne a gidan gwamnati na Sir Kashim Ibrahim, Kaduna a ranar Litinin.
Ya kara da cewa, har yanzu ana ci gaba da gudanar da aikin ceto tare da kwashe dimbin wadanda suka jikkata zuwa asibitin koyarwa na Barau Dikko.
Sanarwar ta kara da cewa, mataimakiyar gwamnan ta jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa yayin da ta yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu.