Sojojin Nijeriya tare da hadin gwiwar gidauniyar Ukan Kurugh sun gudanar da taron masu ruwa da tsaki na kafafen sada zumunta na kwana daya a jihar kebbi mai taken: “Kafafen sada zumunta a matsayin Ingantacciyar hanyar don Inganta Dangantakar Jama’a da Sojoji” wanda a aka gudanar a Saffa da ke Birnin Kebbi.
An shirya taron karawa juna sani ne da nufin dinke barakar da ke tsakanin Sojoji da kungiyoyin farar hula da kuma fadakar da mahalarta taro a kan ayyukan hadin kai da ayyukan soja da rundunar sojojin Nijeriya ta kaddamar a jihohin Arewa maso Yamma baki daya.
- Ambaliya: NEMA Ta Bada Tallafin Kayayyakin Agaji Ga Mutane 22,202 A Kebbi
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Jami’an Kwastam 2 A Kebbi
Ku tabbatar cewa kun gudanar da binciken gaskiya kafin yada duk wani labari don gujewa labaran karya a shafukan sada zumunta,” Cewar jami’in CITAD ya yin taron masu ruwa da tsaki a shafukan sada zumunta a jihar Kebbi.
A nasa jawabin babban bako na musamman, babban kwamandan runduna ta 8 a Nijeriya da ke Sokoto, Manjo Janar Godwin Mutkut, ya bayyana cewa taron karawa juna ilimi ya yi daidai da bukatar babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Taured Lagbaja.
“Mayar da Sojojin Nijeriya zuwa ingantacciyar horarwa, kayan aiki da kwarin gwiwa don cimma nauyin da kundin tsarin mulki ya dora mana” – Lagbaja