Rundunar sojin sama ta Operation Whirl Punch ta lalata ma’ajiyar makaman ‘yan ta’adda da ke Palele a Jihar Neja.
Daraktan yada labarai na rundunar, Air Vice Marshal Edward Gabkwet ne, ya bayyana hakan, inda ya ce hare-haren da aka kai ta sama a ranar 15 ga Maris, 2024, sun biyo bayan bayanan sirri da suka na gano ma’ajiyar makaman ‘yan ta’adda a Gabashin Palele, a Jihar Neja.
- An Rufe Makarantu A Sudan Ta Kudu Saboda Tsananin Zafi
- Tsadar Rayuwa: Gwamnatin Kaduna Za Ta Kashe Naira Biliyan 11.4 Wajen Bayar Da Tallafi
“Ana kyautata zaton makaman na da alaka da lalata a wajen na wani kasurgumin dan ta’adda ne da ake nema ruwa a jallo.
“Ko shakka babu wadannan hare-haren sun dakile karfin ‘yan ta’addan da ke kai hare-hare kan mutanen da ba su ji ba su gani, musamman a jihohin Kaduna da Neja. “in ji shi.
Kakakin rundunar sojin saman ya ba da tabbacin cewa dakarun da sauran jami’an tsaro za su ci gaba sintiri tare da kai samame don dakile ‘yan ta’adda.
Ya kuma yi kira da a taimakawa da rundunar da bayanai game da ayyukan ‘yan ta’adda da sauran miyagun laifuka a jihar.