Rundunar Sojin Sama ta ƙasa (NAF) ta daƙile harin da ’yan ta’adda suka shirya kai wa sansanin Sojoji a Rann, jihar Borno, tare da kashe da dama daga cikinsu yayin da suke tserewa.
Mai magana da yawun NAF, Ehimen Ejodame, ya bayyana cewa dakarun saman ƙarƙashin Operation Haɗin Kai (OPHK) sun hana harin ne da safiyar 8 ga Agusta, 2025, ta hanyar samun bayanan leƙen asiri da kai farmaki daga sama.
- Tashin Gurneti Ya Hallaka Yara Uku A Borno
- Sojoji Sun Kama Mai Yi Wa Boko Haram Safarar Man Fetur A Borno
An gano tarin ƴan ta’adda da ke gudu bayan samun bayanan sirri, sannan aka fatattake su da makamai na musamman, inda aka hallaka da dama daga cikinsu.
Ejodame ya ce wannan matakin gaggawar da aka ɗauka ya dawo da zaman lafiya a yankin, yana kuma nuna jajircewar NAF wajen kare Sojoji da shawo kan barazanar ƴan ta’adda cikin hanzari.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp