Rundunar sojojin ‘yantar da jama’ar kasar Sin, da rundunar ‘yan sandan kasar masu dauke da makamai, da dakarun sa-kai na cikin gida sun aike da dakaru domin shiga ayyukan ba da agajin gaggawa a yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa a kasar Sin.
A baya-bayan nan ne aka tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya a gabashi, da arewaci, da arewa maso gabas na kasar Sin, lamarin da ya haddasa ambaliya da sauran ibtila’i na zaftarewar kasa da suka yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyi.
Rundunar ‘yan sanda masu dauke da makamai ta birnin Beijing ta aike da jami’ai da sojoji sama da 2,000 don taimaka wa ayyukan ba da agajin, inda aka kwashe sama da mazauna yankin da abin ya shafa 4,100 tare da kai akwatunan kayayyakin agaji fiye da 3,000 da tsakar ranar yau Talata. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp