Dakarun Sojin Kasar Somaliya (SNA) da ke samun goyon bayan mayakan sa kai da ake wa lakabi da Ma’awisley, sun kashe mayakan al-Shabab sama da 100, tare da ‘yantar da kauyuka sama da 20, a wani samamen da suka kai a wasu jihohin yankuna biyu a ranar Lahadin da ta gabata.
Ma’aikatar yada labarai da al’adu da yawon bude idon kasar, ta ce an gudanar da ayyukan ne a jihohin Galmudug da Hirshabeelle da kuma Kudu-maso-Yamma.
- An Ceto Mutane Fiye Da 650 Da Girgizar Kasa Da Ta Auku A Lardin Sichuan Na Kasar Sin
- Bikin Tsakiyar Kaka Na 2022 Da CMG Ya Nuna Ya Samu Yabo Sosai Daga Masu Kallo A Gida Da Waje
Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta ce “Kungiyar ta’addancin na amfani da wadannan garuruwa a matsayin tunga wajen shirya hare-haren ta’addancinsu da bama-bamai da ‘yan kunar bakin wake a sassa daban-daban na Somaliya.”
Ta ce ‘yan ta’addar sun yi wa fararen hular yankin da suka yi garkuwa da su kisan gilla, tare da lalata dukiyoyinsu.
Gwamnatin kasar ta bayyana kudirinta na fatattakar kungiyar ta’addanci ta Al-Shabab, wadda ke zama barazana ga al’ummar Somaliya, daga maboyarta.
Ma’aikatar ta ce “Kungiyar ta’addancin ta shafe shekaru goma tana aikata munanan laifuka kan fararen hula a garin da suke iko da su.”
Kungiyar da ke fafutukar hambarar da gwamnatin kasar na fuskantar matsananciyar matsin lamba da farmaki daga dakarun gwamnati da ke samun goyon bayan mayakan sa kai da ke neman fatattakar su daga yankin Hiran da ke tsakiyar kasar Somaliya.
An fatattaki Al-Shabab daga Mogadishu a shekarar 2011 amma har yanzu kungiyar ta’addancin na iya kai hare-hare kan cibiyoyin gwamnati, otal-otal, gidajen abinci, da wuraren taruwar jama’a.