Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa kuma ɗan gwagwarmaya, Omoyele Sowore, ya kai ƙarar Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS), kamfanin Meta, da X Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Lauyoyinsa sun ce an shigar da ƙarar ne don hana abin da suka kira “take haƙƙin ‘yancin faɗar albarkacin baki” a kafafen sada zumunta.
- Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo
- DSS Ta Maka Sowore, Facebook Da X A Kotu Kan Wallafa Rubutu Game Da Tinubu
Lauyinsa, Tope Temokun, ya ce: “Idan hukumomin gwamnati za su riƙa umartar manyan kafafen sadarwa da su hana mutane damar yin magana, to babu wani ɗan Nijeriya da zai tsira. Za s hana mutane bayyana ra’ayoyinsu saboda son ran masu mulki.”
Ya ƙara da cewa: “Tsangwama ba ta da tushe a dimokuraɗiyya. Kundin tsarin mulkin Nijeriya ya bai wa kowa ‘yancin faɗar albarkacin baki, kuma babu wata hukuma da ke da ikon soke wannan haƙƙi.”
Lauyoyin Sowore sun ce Meta da X bai kamata su amince da umarnin tsangwama ba, domin hakan zai sanya su cikin masu tauye ‘yancin jama’a.
Sun jaddada cewa dole ne manyan kafafen sada zumunta su kare ‘yancin yin magana.
Sun kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya, ‘yan jarida, da masu fafutukar kare haƙƙin bil’adama su tashi tsaye don hana abin da suka kira yunƙurin mayar da Nijeriya “mulkin kama-karya a intanet.”
Lamarin ya biyo bayan wa’adin sati guda da DSS ta bai wa Sowore da ya goge wasu wasu rubuce-rubuce game da Shugaba Bola Tinubu, wanda ya ƙi amincewa.
Hakan ya sa hukumar ta shigar da shi ƙara a kotu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp