Kasar Spain ta lashe kofin Duniya na kwallon mata da aka buga a kasashen Australia da New Zealand.
Ta samu nasarar lashe kofin ne bayan ta doke kasar Ingila a wasan karshe na kofin Duniyar a Sydney.
Kyaftin din kasar Spain Olga Carmona ce ta jefa kwallo kafin aje hutun rabin lokaci.
Kuma kwallon daya tilo ta kasance dalilin lashe kofin Duniya na kwallon mata ga kasar Spain a karo na farko a tarihin kasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp