A wannan kakar wasan dai an samu ‘yan wasan Afirka da dama da suka samu canjin kungiya a Nahiyar Turai kuma tuni sun fara bugawa sababbin kungiyoyinsu wasa a matakan wasannin cikin gida da kuma na Nahiyar Turai da aka fara a wannan makon.
A satin da ya gabata ne aka dawo wasannin manyan gasannin Turai bayan hutun da aka tafi na wasannin tawagogin kasashe, yanzu ‘yan wasan Afirka da suka canja kungiya ne suke kokarin ganin sun fara da kafar dama.
- Sama Da Kasashe Da Hukumomin Kasa Da Kasa 70 Sun Ba Da Tabbacin Halartar Bikin CIIE Karo Na 7
- Mun Samu ‘Yan Takara Masu Tu’ammali Da Miyagun Kwayoyi – Hukumar Zaben Kaduna
Dan wasa Victor Oshimhen wanda ya zura kwallo a wasan da Nijeriya ta lallasa Benin da ci uku da nema a wasan neman gurbin shiga Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka yana daya daga cikin manyan ‘yan wasannin da suka canja kungiya kuma tuni ya fara da zura kwallo a sabuwar kungiyarsa ta Galatasaray.
Dan wasan gaban ya koma Galatasary ne bayan kai-komo da aka sha a game da makomarsa har ta kai yawancin manyan gasannin Turai sun rufe kasuwancin ‘yan wasa bai samu komawa daya daga cikin kungiyoyin Chelsea ko Al-Hilal ta Saudiyya ba.
An ci kasuwar ‘‘yan wasa da dama a kakar bana, ciki har da Gasar Saudi Pro League da ta sake kwasar ‘yan wasa, sannan tsohon dan wasan Nijeriya Bictor Moses wanda ya koma buga wasa a kungiyar Luton Town da ke Ingila.
Victor Osimhen (Napoli zuwa Galatasaray)
Tun da farko an samu tsaiko a kan makomar dan wasa Bictor Osimhen saboda zaman tankiyar da aka samu tsakanin dan wasan da Napoli, har ta kai ya koma Turkiyya duk da cewa tun farko an yi hasashen dan wasan zai koma kungiyar PSG ta Faransa ne ko daya daga cikin manyan tawagogin premier ta Ingila ko kuma Saudiyya.
A karshe dai yanayin tsaikon da aka samu ya sa dole dan wasan mai shekara 25 ya bi sahun wani gwarzon dan wasan na Afirka Didier Drogba, wanda shi ma ya buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Galatasary kuma ya sanya hannu a kwantiragin aro na shekara daya.
A cikin kwantiragin an amince cewa a tsakiyar kaka wato a Janairu idan wata kungiya ta yi zawarcinsa zai tafi, amma abubuwa ba su tafi kamar yadda yake so ba, dole zai koma Napoli duk da cewa dangantaka ta riga ta yi tsami tsakanin dan wasan da kungiyar ta Napoli.
Tuni dan wasan ya fara zura kwallo a kungiyar ta Galatarasay a wasansa na farko a kungiyar kuma ana sa ran tauraruwarsa za ta haska a kungiyar ganin cewa ‘yan wasan Afirka suna tabuka abin a zo a gani a kasar Turkiyya.
Wilfried Zaha (Galatasaray zuwa Lyon)
Abin mamaki, shima sai a sa’o’in karshe ne aka samu nasarar sayar da dan wasan na Ibory Coast zuwa kungiyar Lyon ta Faransa a matsayin aro na kakar wasa daya, duk da cewa tun farko dan wasan ya so komawa kasar Ingila domin ci gaba da buga gasar firimiya.
Dan wasan mai shekara 31 ya lashe Gasar Turkiyya a kakar bara, amma kuma da zura kwallaye 10 da ya yi a wasanni 42 da ya buga ciki har da zura kwallo a ragar Manchester United a Gasar Zakarun Turai a karshe-karshen kakar ba a cika fara wasa da shi ba.
Kawo yanzu dai tsohon dan wasan na Crystal Palace zai so ya samu lokaci sosai domin nuna bajintarsa a Faransa, inda ake tunanin zai zama abin koyi na matashin dan wasan gaban Nijeriya Gift Orban, wanda yake buga wasa a kungiyar.
Yanzu dai ana jira a gani bayan rashin samun nasara a kasar Turkiyya, shin Zaha zai dawo ya ci gaba da rawar gaban hantsi a Faransa kamar yadda aka saba ganinsa a tsohuwar kungiyarsa ta Crystal Palace ta Ingila?
Serhou Guirassy (Stuttgart zuwa Borussia Dortmund)
Har yanzu magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund ba su fara ganin dan wasan gabansu Guirassy a filin wasa ba saboda rauni da ya ji a wasannin sharar fage kafin a fara buga kakar wasa ta bana. Amma dan wasan na kasar Guinea wanda ya zura kwallaye 28 a wasanni 28 da ya buga a kakar bara sun taimaka wa kungiyar samun gurbin a Gasar Zakarun Turai, yanzu ya dawo atisaye sosai, kuma zai fara wasa a wannan watan.
Dan wasan wanda ya fi dadewa a kananan gasanni wato na rukuni na biyu a kasashen Faransa da Jamus, ya kasance wanda ya fi zura kwallaye na biyu a gasannin a kakar wasa ta 2023 zuwa 2024 bayan Harry Kane.
Daraktan Wasanni na Dortmund Sebastian Kehl ya bayyana dauko dan wasan a farashin fam miliyan 15 ($11.4m) a matsayin kasuwanci mai kyau inda ya ce Serhou cikakken dan wasan gaba ne, wanda yake da matukar hadari wajen zura kwallo.
Noussair Mazraoui (Bayern Munich zuwa Manchester Utd)
Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Erik ten Hag ya dauko daya daga cikin zaratan ‘‘yan wasan da ya yarda da su wato Noussair Mazraoui ne domin karfafa tsaron tawagar a bangaren baya.
Dan wasan mai shekara 26 yana cikin ‘‘yan wasan Maroko da suka kai wasan kusa da karshe a gasar cin kofin duniya ta 2022 kuma yana cikin ‘‘yan wasa biyu da kungiyar ta dauko a kan fan miliyan 60 ($45.6m), tare da dan wasan bayan Netherland, Matthijs de Ligt.
Bayan komawarsa kungiyar ta Manchester United, Mazraoui ya bayyana cewa mai koyarwa Erik ten Hag yana cikin wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen zamowarsa kwararren dan kwallo, shi ya sa yake farin cikin sake haduwa da shi.
Ba dukkan ‘‘yan wasan Ajad da Ten Hag ya kawo Old Trafford ba ne suka samu nasara, domin dan wasa Antony bai samu nasara ba kuma ana ganin Mazraoui zai iya taimakon kocin nasa wajen rage masa zafi a Manchester United.
Kelechi Iheanacho (Leicester City zuwa Sebilla)
Sebilla, kungiyar Spain ta maye gurbin wani dan wasan Afirka ne dan kasar Maroko Youssef En-Nesyri da ya koma Fenerbahce a cikin watan Agusta, kuma kungiyar ta Sebilla ta dauko Iheanacho a kan kwantiragin shekara biyu.
Tsohon dan wasan na Manchester City, mai shekara 27 ya zura kwallo 61 a wasa 232 da ya buga a zamansa na shekara bakwai a Leicester, inda ya lashe gasar kofin kalubale wato FA a 2021, sannan yana cikin ‘yan wasan da suka taimaka wa kungiyar wajen dawo da ita gasar premier a bana.
Sebilla ta kare a mataki na 14 ne a kakar bara, wanda shi ne mafi muni tun bayan dawowarta Gasar La Liga a 2001, sannan yanzu Iheanacho zai so ya kara wa kungiyar armashi da zura kwallaye domin dawo da kungiyar matakin da take a Nahiyar Turai.
Jordan Ayew (Crystal Palace zuwa Leicester)
Tun bayan da Iheanacho ya koma Sebilla, sai kungiyar Leicester shiga kasuwa kuma ta dauko dan wasan kasar Ghana, Ayew, daga Crystal Palace kuma dan wasan mai shekara 32 ya shiga yarjejeniya shekara biyu a kan Fan miliyan 5.
Ayew ya yi shekara shida a kungiyar Crystal Palace, inda ya zura kwallo 23 a wasanni 212 da ya buga, sannan dan wasan ya bayyana cewa duk da cewa ya kai shekara 32 yanzu, amma kullum yana sake koyon abubuwa domin kara kwarewa.
Duk da cewa tawagar Black Stars ta Ghana maki daya kacal ta samu a wasanni biyu na neman gurbin shiga Gasar Cin Kofin Afirka ta 2025, Ayew zai yi kokarin ganin ya yi amfani da kwarewarsa wajen tabbatar da Leicester City ta ci gaba da zama a gasar premier.