Mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Dino Melaye, ya ce subutar bakin da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya yi a lokacin kaddamar da yakin neman zabensa a garin Jos, babban birnin Jihar Filato, alamu ne da ke nuna cewa bai cancanci ya shugabanci kasar nan ba.
Melaye ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce “Addu’ar da Asiwaju ya yi wa jam’iyyar PDP a wajen gamgamin yakin neman zabensa a garin Jos hakan ya nuna a zahiri bai cancanta ya nemi takarar kujerar shugaban kasa ba.”
- Kotu Ta Kori Karar Da Maina Ya Shigar Kan Ministan Harkokin Cikin Gida Da Wasu
- Lalong Ya Yi Allah-wadai Da Kashe-kashen Da Aka Yi A Filato, Ya Bukaci A Gurfanar Da Masu Laifin
Melaye, ya bukaci masu kada kuri’a a kasar nan da su yi duba na tsanaki ga ‘yan takarar na shugaban kasa a kan sikeli domin su tantance cancantar su da kuma tantance jam’iyyun da suke yin takarar a cikinsu.
Melaye ya kara da cewa, “‘Yan kasar nan a yanzu suna da babbar dama, musamman domin su kaucewa maimaita shugabanci irin na gwamnatin Buhari, wanda kuma yake yawan tafiye-tafiye zuwa ketare.”
Ya kuma yi nuni da cewa, shekaru sun dabaibaye Asiwaju, maganar iliminsa na zamani, wasu ‘yan Nijeriya na ta yin muhawara akai.
Dino ya yi nuni da cewa, “Abin kunya ne ga Asiwaju yadda a makon da ya gabata da kyar da jibin goshi ya samu goyon bayan kungiyar Yarabawa zalla ta Afenifere.
“Wannan ya nuna a zahiri Asiwaju bai da wani karfi na siyasa a yankin na Yarabawa.
“A irin halin da Asiwaju yake ya nuna a gangamin a garin Jos zai iya samo wa kansa matsala da kuma rashin sanin makomar da kasar za ta tsinci kanta a ciki idan har ya zama shugaban kasar nan a 2023.”