• English
  • Business News
Monday, August 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

SULEJA – An Ci Moriyar Ganga (3)

by Mairo Muhammad Mudi
3 months ago
in Bakon Marubuci
0
SULEJA – An Ci Moriyar Ganga (3)
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Yayin shirin kidayar jama’a ta shekarar 2006, Tsohon Shugaban Hukumar Kidayar Jama’a ta Kasa, Cif Samuila Danko Makama, ya gudanar da aikin wayar da kai a Suleja. A cikin jawabin nasa, ya bayyana yadda kimar yawan jama’ar garin yake na musamman, saboda kusancinsa da Babban Birnin Tarayya. A martaninsa ga wannan jawabi, Sarkin Suleja, Malam Muhammadu Awwal Ibrahim, ya ce; “Duk sanda Abuja ta yi tari, Suleja sai ta kamu da mura.”

Mai Martaba ya fadi gaskiya, domin a lokacin, an fara rusa gine-ginen da ba bisa ka’ida ba a Gwagwa, Karmo, Jiwa da kewaye, kuma yawancin wadanda abin ya shafa, sun kwarara zuwa Suleja. Duk da haka, babu wani taimako na musamman da aka bai wa garin domin daukar wannan nauyi. Wannan ya kai ga wata cikakkiyar wallafa a jaridar Daily Trust a ranar 31 ga Oktoba, 2006, wanda Malam Nasiru Imam ya rubuta, mai taken: ‘Abuja Grows, Suleja Groans’.

  • Wakilin Sin Ya Soki Yadda Amurka Ke Tafiyar Da Kudurin Takunkuman Sudan Ta Kudu
  • Zulum Ya Ba Da Tallafin Karatu Ga Mata ‘Yan Asalin Jihar Da Suka Samu Maki 250 A JAMB

Taken binciken rubutun digirina na biyu a Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria (ABU), ya kasance: Tasirin Abuja ga ci gaban Suleja. Daga binciken da na yi a Ma’aikatar Kudi ta Jihar Neja, na gano cewa; a shekarar 1994, fiye da shekara 30 da suka wuce, jimillar kudin da jihar ta samu daga hanyoyin ciki, bai wuce Naira miliyan 64 ba. Sai dai, Suleja kadai ta bayar da Naira miliyan 24, wanda ya kai kashi 37.8 cikin 100. A wancan lokaci, albashina a matsayin ma’aikaci a matakin Lebel 09 a Hukumar FCDA, bai kai Naira 1,000 ba.

Ka’idar biyan haraji ita ce, domin samar da ababen more rayuwa da ayyuka ga al’umma. Amma dukkanin ma’aikatan Abuja da iyalansu da ke zaune a Suleja, suna amfana da asibitoci, makarantun gwamnati da sauran ayyuka da ke garin Suleja. Sai dai harajinsu, wanda ma’aikatansu ke cirewa daga albashi, ba a mayar da shi ga gwamnatin da ke samar da wadannan ayyuka a Suleja ba.

Mutanen Suleja, sun jima suna kira da a dawo da harajin PAYE na ma’aikatan Abuja da ke zaune a Suleja, saboda suna da yakinin cewa; hakan zai sa Gwamnatin Jihar Neja ta fi kula da Suleja. An amince da hakan, sannan kuma yanzu ana karbarsa a boye-boye, amma babu wani canji da aka gani a kasa.

Labarai Masu Nasaba

Yaushe Shugaban Kasa Zai Ba ‘Yan Matan Yobe Nasu Kyaututtukan

Daga Sawaba Zuwa Asara: Baje Kolin Kasuwancin Siyasa A Kano – Auwalu Anwar

Yanzu haka, akalla ana iya karbar sama da Naira miliyan 100 daga wannan PAYE a kowane wata. Wasu hanyoyin samun kudaden shiga, sun hada da haya na kasa (ground rent), harajin haya (tenement rate), da harajin wuraren kasuwanci. Har ma da noma, ana sa wa haraji a Suleja, duk da cewa; gwamnan jihar manomi ne. Ya dace gwamnati ta tabbatar da cewa; ana samar da kayayyakin more rayuwa masu inganci a Suleja, ko da don a samu karin haraji ne.

Idan har gwamnatin tarayya ba ta yaba da sadaukarwar da Suleja ta yi ba, to akalla Gwamnatin Jihar Neja; ya kamata ta fi mayar da hankali wajen samar da ci gaba a Suleja, domin karrama gudunmawar da garin ke bayarwa wajen samun kudaden shiga ga jihar. Har ila yau, adalci ne a dawo da abin da aka karba ta hanyar ayyuka ga al’umma.

Tsohon Gwamna, Babangida Aliyu ya ce; gwamnatinsa ta gina titin cikin gari na kilomita 10 a kowace karamar hukuma. Amma ba a kai wa Suleja kilomita uku ba. Titin Gwazunu da aka ce an gyara, bai kai shekara biyu ba ya lalace. Aliyu kuma ya zo da burin aikin Twin City, ciki har da aikin titin Madalla mai layi biyu, a cikin bashi da aka fito da shi. Amma aikin da bashin duk sun bace bat kamar iska.

Gwamnatin yanzu ta sanar da shirin samar da tituna na tsawon kilomita 50 a kowanne daga cikin garuruwa uku: Bida, Kontagora da kuma Suleja. An kaddamar da aikin a sauran wuraren amma ban da Suleja ba.

Watakila aikin titin da aka fara shi ne, wanda ake gina magudanan ruwa marasa inganci a gefen titin Maje zuwa Madalla da kuma hanyar Kaduna. Wannan abin takaici ne. Abu mafi muni shi ne, tsoffin magudanan ruwa da Gwamna Kure ya gina fiye da shekaru 20 da suka wuce, wadanda yanzu ake maye gurbinsu, sun fi wadanda ake ginawa yanzu inganci.

Titin Maje zuwa Madalla na daga cikin manyan titunan tarayya, ‘Trunk A-124’. Ma’ana, gwamnatin jiha, na sa ran gwamnatin tarayya za ta biya su bayan shekara 10. Amma ta yaya aiki marar inganci irin haka zai cancanci a biya kudinsa? Idan har gwamnatin yanzu ta ki gyarawa, ta ci gaba da biyan kwangilar wanda ko sunansa ba a so a sani, duk da gurbataccen aikin da korafi masu yawa, hakan yana nuna cewa; abin da ta fi mayar da hankali a kai shi ne kudi, ba aiki ko jin dadin jama’a ba. haka zalika kuma, wannan gwamnatin ba ta damu da matsalolin da za su bar wa gwamnati mai zuwa ba.

Masu gidaje, yawancinsu ‘yan asalin garin wadanda aikin ke shirin shafar su ne, don haka dole ne a biya su diyya tare da sake musu matsugunai. Amma har yanzu, babu wani shiri na sake matsugunan ko kididdigar diyya da aka sanar a Suleja. Amma an gudanar da hakan a wasu al’ummomi a cikin jihar.

Babu shakka, ikon gwamnati ya shafi dukkanin Jihar Neja, ba Suleja kadai ba. Amma Hassan da Hussaini duka suna da hakkin da ya caccanta a ba su. Sai dai, ba dai-dai ba ne a tauye hakkin Hassan don a amfanar da Hussaini. A bayyane yake karara, inda ake samun kudin shiga a Jihar Neja, ba can ake yi da su ba. A gaggauta gyara tunda lokaci bai kure ba.

Alhamdulillah!


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Suleja
ShareTweetSendShare
Previous Post

Gwamna Yusuf Ya Bada Hutu A Ranar Litinin Domin Addu’o’i Ga ‘Yan Wasan Kano 22

Next Post

NDLEA Ta Cafke Masu Tura Alhazai Saudiyya Domin Safarar Hodar Iblis Zuwa Kasar

Related

Yaushe Shugaban Kasa Zai Ba ‘Yan Matan Yobe Nasu Kyaututtukan
Bakon Marubuci

Yaushe Shugaban Kasa Zai Ba ‘Yan Matan Yobe Nasu Kyaututtukan

3 days ago
Hoton Kwankwaso da Ganduje da Shekarau
Bakon Marubuci

Daga Sawaba Zuwa Asara: Baje Kolin Kasuwancin Siyasa A Kano – Auwalu Anwar

5 days ago
Manufofin Hulda Da Kasashen Wajen Da Nijeriya Ke Bukata
Bakon Marubuci

Manufofin Hulda Da Kasashen Wajen Da Nijeriya Ke Bukata

1 week ago
Hadarin Da Ke Kunshe Da Jin Bangare Daya Na Labari
Bakon Marubuci

Hadarin Da Ke Kunshe Da Jin Bangare Daya Na Labari

1 month ago
Yawaitar Al’umma: Martanin Karl Marx Ga Rabaran Malthus
Bakon Marubuci

Yawaitar Al’umma: Martanin Karl Marx Ga Rabaran Malthus

2 months ago
Dabi’a: Yadda Ake Gini Da Rusa Ta 
Bakon Marubuci

Dabi’a: Yadda Ake Gini Da Rusa Ta 

2 months ago
Next Post
NDLEA Ta Cafke Masu Tura Alhazai Saudiyya Domin Safarar Hodar Iblis Zuwa Kasar

NDLEA Ta Cafke Masu Tura Alhazai Saudiyya Domin Safarar Hodar Iblis Zuwa Kasar

LABARAI MASU NASABA

Ɗaruruwan Mambobin APC Sun Sauya Sheka Zuwa ADC A Sokoto

August 24, 2025
Ƴansanda Sun Kama Wani Gawutaccen Ɗan Fashi Da Garkuwa Da Mutane A Nasarawa

Ƴansanda Sun Kama Wani Gawutaccen Ɗan Fashi Da Garkuwa Da Mutane A Nasarawa

August 24, 2025
Za A Bude Cibiyar Watsa Labarai Game Da Bukukuwan Nasarar Yaki Da Harin Japan 

Za A Bude Cibiyar Watsa Labarai Game Da Bukukuwan Nasarar Yaki Da Harin Japan 

August 24, 2025
An Kaddamar Da Makon Fina-finai Da Shirye-shiryen Talabijin Na SCO A Qingdao

An Kaddamar Da Makon Fina-finai Da Shirye-shiryen Talabijin Na SCO A Qingdao

August 24, 2025
CMG Za Ta Gabatar Da Bikin Faretin Soja Na Beijing Cikin Harsuna 85 Ga Duk Fadin Duniya 

CMG Za Ta Gabatar Da Bikin Faretin Soja Na Beijing Cikin Harsuna 85 Ga Duk Fadin Duniya 

August 24, 2025
Akwai Katin Zaɓe Fiye Da Dubu 367 Da Ba A Karɓa Ba A Kano – INEC

Akwai Katin Zaɓe Fiye Da Dubu 367 Da Ba A Karɓa Ba A Kano – INEC

August 24, 2025
An Kaddamar Da Gini Mara Fitar Da Hayakin Carbon Irinsa Na Farko A Duniya

An Kaddamar Da Gini Mara Fitar Da Hayakin Carbon Irinsa Na Farko A Duniya

August 24, 2025
Kasar Sin Ta Gudanar Da Bita Na 3 Na Bikin Cika Shekaru 80 Da Samun Nasara A Yakin Kin Harin Japan

Kasar Sin Ta Gudanar Da Bita Na 3 Na Bikin Cika Shekaru 80 Da Samun Nasara A Yakin Kin Harin Japan

August 24, 2025
Ya Kamata A Kiyaye Sahihin Tarihi Da Rike Gaskiya

Ya Kamata A Kiyaye Sahihin Tarihi Da Rike Gaskiya

August 24, 2025
Tanko Yakasai Ya Nuna Takaici Kan Rashin Samar Da Kamfanin Sarrafa Fata A Kano Kamar Na Legas

Tanko Yakasai Ya Nuna Takaici Kan Rashin Samar Da Kamfanin Sarrafa Fata A Kano Kamar Na Legas

August 24, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.