Sarkin Sokoto kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Arewa, Mai Martaba Sultan Sa’ad Abubakar na II, ya yi kira ga gwamnonin jihohin Arewa 19 da su saurari masu sukarsu sosai kuma su yi amfani da ra’ayoyi masu amfani don ƙarfafa shugabanci a duk faɗin yankin.
Ya yi gargaɗin cewa, yin watsi da sukar na iya rage yunƙurin magance ƙalubalen yankin, musamman rashin tsaro, talauci, da taɓarɓarewar tattalin arziki.
- Jami’an Tsaro Sun Daƙile Harin Lakurawa, An Harbe Ɗaya A Kebbi
- Gwamnatin Kano Ta Fara Ɗaukar Matakan Daƙile Dawowar Masu Achaba
Da yake jawabi a ranar Litinin a taron haɗin gwiwa na Ƙungiyar Gwamnonin Arewa da sarakunan gargajiya a Kaduna, Sultan ya jaddada cewa babu wani shugaba da ke neman amincewar jama’a amma kuma ya juya musu baya da gangan bayan ya hau mulki.
Sultan ya yi takaicin cewa, galibi ana zargin gwamnoni da rashin aiki yadda ya kamata, duk da matsin lambar da suke fuskanta.
“Kullum ina jin ba daɗi idan na ji an ce, gwamnan ba ya son yin komai ko kuma shugaban ƙasa ba ya son yin komai. Babu gwamna, babu shugaban ƙasa da zai nemi kuri’un jama’a, kuma idan ya hau mulki, abin da zai yi kawai, shi ne ya juya wa jama’a baya,” in ji shi.
Ya yi kira ga gwamnonin da su “saurari masu suka, su saurari sukar, sannan su yi gyare-gyare a lokacin da ake buƙata,” yana mai lura da cewa ra’ayoyin da aka bayar na gaskiya na iya jagorantar yanke shawara mafi kyau.














