Mai taimakawa ministan harkokin wajen kasar Syria Ayman Soussan, ya ce kasar Sin ta kuduri aniyar kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyyar da duniya baki daya, kuma tana taka muhimmiyar rawa tare da yin tasiri a harkokin kasa da kasa.
Ayman Soussan ya bayyana hakan ne a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a kwanan baya a birnin Damascus, babban birnin kasar Syria, inda ya bayyana cewa, kasar Sin na mutunta dokokin kasa da kasa da ikon mallakar dukkan kasashe, kuma tana adawa da ra’ayin nuna danniya ko babakere, da fatan dukkan kasashe za su iya samun tsaro da wadata.
Musamman ma ya yi nuni da cewa, shawarar da kasar Sin ta gabatar na warware rikicin kasar Ukraine ta hanyar siyasa da kokarin shiga tsakani da take yi na mayar da huldar jakadanci tsakanin Saudiyya da Iran, na da nufin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Baya ga haka, ya kara bayyana cewa, Amurka da wasu kasashen yamma sun yi ta kokarin haifar da shakku a tsakanin kasashen yankin, da nufin kara tada zaune-tsaye, ta yadda za a yi amfani da muradun Amurka na nuna danniya ko babakere, lamarin da ya kawowa al’ummar kasashen yankin wahala. (Mai fassara: Bilkisu Xin)