Bayan kammala bikin baje kolin hajojin da ake shigowa da su kasar Sin ko CIIE karo na 7 a jiya Lahadi, wasu alkaluma sun shaida yadda baje kolin na CIIE ya haifar da tarin sakamako, inda aka yi fatan hada hadar cinikayya mai nasaba da baje kolin za ta kai dalar Amurka biliyan 80.01 a shekara, karuwar da ta kai ta kaso 2.0% sama da ta baje kolin da ya gabata.
A wannan karo, masu baje hajoji 3,496 daga kasashe da yankuna 129 sun hallara, ciki kuwa har da wasu daga manyan kamfanonin duniya mafiya girma 500, da kusoshin manyan masana’antun kasa da kasa da a wannan karo yawan su ya kafa tarihi.
- Yadda Gwamna Dauda Ya Inganta Cibiyoyin Kiwon Lafiya A Jihar Zamfara
- Okawa Bai Taimake Ni Da Kuɗin Jihar Delta Don Na Yi Kamfe A 2023 Ba – Atiku
A halin da ake ciki, salon kasar Sin na bude kofa ga sassan waje ya karkata daga samar da kayayyaki, da fitar su daga gidaje zuwa masana’antu, zuwa tsarin bude kofa na jagoranci.
Tsarin CIIE da manufofin shiga kasar Sin ba tare da bukatar Biza ba, sun baiwa kasar Sin damar kara dinkewa da sauran sassan duniya, da fadada hade tattalin arzikin ta da na sauran sassan kasa da kasa.
Bude kofa wani ginshiki ne na musamman a salon kasar Sin na zamanantarwa, kuma wata haja ce da ake matukar bukata, wadda Sin ke samarwa duniya. Kuma hakan ne ya sanya kamfanonin kasashen waje ke daukar manufar shiga kasar Sin a matsayin wani buri mai dogon zango. (Mai fassara: Saminu Alhassan)