A ran 26 ga wata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada a ganawarsa da sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken da ke ziyara a kasar cewa, kamata ya yi kasashen biyu su kasance abokan hulda, maimakon abokan gaba, su taimaki juna cimma nasara, maimakon cutar da juna, su nemi cimma matsaya guda da ajiye bambance-bambance, maimakon shiga muguwar gasa, da kuma fada da cikawa, maimakon yin magana da baki biyu.
Me ya sa Amurka a ko da yaushe take furta kalma amma sai ta aikata sabanin abin da ta furta? Li Haidong, shehun malami a jami’ar ilmin harkokin wajen kasar Sin, ya bayyana cewa, yin magana da baki biyu, wata babbar cuta ce ta gwamnatin Amurka a lokacin tafiyar da dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin. Ban da wannan kuma, bana shekarar zabe ce a Amurka, sha’anin siyasa na cikin gida a Amurka ya kara ta’azzara, kana sauye-sauyen da suka shafi alkiblar manufofin kasar Sin sun karu, dukkansu sun yi tasiri kan manufofin gwamnatin Amurka game da yadda take mu’amala da kasar Sin. Idan an yi tunani mai zurfi kuma, an gano cewa, Amurka na bukatar yin hadin gwiwa da kasar Sin yayin da kuma take yunkurin dalike ci gaban kasar Sin, lamarin da ke nuna cewa, wasu mutanen Amurka suna da gajeren tunani, da yin kuskuren daukar kasar Sin a matsayin “babbar abokiyar hamayyarta bisa manyan tsare-tsare”, da kuma babban rashin fahimtar manufar bunkasuwar kasar Sin.
- Binciken CGTN: Ba Karfin Samar Da Kayayyaki Na Kasar Sin Ba Ne Ya Wuce Kima, Sai Dai “Kariya Irin Na Amurka”
- Dalilin Da Ya Sa Duniya Ke Bukatar Karfin Sin Na Samar Da Hajoji Masu Alaka Da Makamashi Mai Tsafta
An lura da cewa, yayin da aka yi mu’amala tsakanin manyan jami’an Sin da Amurka a cikin ‘yan shekarun nan, an tattauna batun fahimtar manyan tsare-tsare. A yayin ziyarar ta Blinken a wannan karo, bangaren Sin ya jaddada cewa, kasar Sin kasa ce mai ra’ayin gurguzu da ke bin hanyar samun ci gaba cikin lumana. Kuma ba ta dauke da tunanin hamayya ko yakin cacar baka, dukkan wadannan ba dabi’un kasar Sin ba ne. Wadannan kalamai sun aike da sako karara cewa, manufar ci gaban kasar Sin ita ce samar da ingantacciyar rayuwa ga jama’arta, ba wai ta maye gurbin Amurka ba. Bugu da kari, kasar Sin a ko da yaushe tana kallon dangantakar dake tsakaninta da Amurka bisa ma’aunin kiyaye tushen jin dadin jama’ar kasashen biyu, da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, kana tana tsayawa tsayin daka wajen mutunta juna, zaman tare cikin lumana, da hadin gwiwar samun nasara tare. (Yahaya)