• English
  • Business News
Monday, October 20, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ta Yaya Zan Yi Tattalin Mijina?

by Rabi'at Sidi Bala
1 month ago
Miji

Yadda za ki yi Tattalin mijinki cikin sauƙi da kwanciyar hankali:

Ƴar uwa mace za ta iya tattalin mijinta cikin sauƙi idan ta cire girman kai da ganin ita ta isa, sannan kuma ta sa haƙuri da jajircewa da juriya a duk yadda ta samu kanta tare da yawaita addu’a. Sai dai kamar yadda maza suke da haƙƙi a kan matansu, to haka su ma matan suna da haƙƙi a kan mazajensu, kamar yadda aya ta 227 ta cikin suratul Baƙara ta bayyana.

Sai dai a nan za a dubi yadda mace za ta yi tattalin mijinta ne kamar yadda za mu yi bayani in Sha Allahu. Daga cikin dabarun da mace za ta bi don ta tattali mijinta sun haɗa da:

  1. Nuna masa soyayya a zahiri da ɓoye, da bin umurnin da duk ya yi mata a gabansa ne ko kuma a bayan idonsa ne wanda bai saɓa wa shari’a ba, da yin haƙuri da talaucinsa idan ya kasance talaka ne, da riƙe masa sirrinsa musamman a kan wani aibi da yake da shi, da yin shiru a lokacin da ya fusata har sai ya sauko, da yi masa magana cikin tausasawa da rarrashi.
  2. Yi wa miji kwalliya, da yawan yin tsafta ba tare da zama da ƙazanta ba, da yi wa miji murmushi da sakin fuska, da yin tarayya da shi a lokacin da yake cikin farin ciki ko baƙin ciki, da amsa masa kira a duk lokacin da ya kira ki, da rashin aikata abin da zai fusata shi.
  3. Ki guje wa rashin godiya a kan abin da yake maki na kyautatawa komai ƙanƙantarsa, da gujewa yawan kai masa ƙara ko ta wane ne, da gujewa kai shi ƙara a wajen iyayenki har sai in abin ya zama dole sai an yi hakan, kada ki riƙa yi masa alfahari da tinƙaho da kyawunki ko dukiyarki idan kin zama kin fi shi kuɗi.
  • Hanyoyi Goma Sha Daya Da Mace Za Ta Bi Domin Janyo Hankalin Mijinta
  • Ki Bar Auna Yadda Mijinki Yake Miki Da Yadda Wani Yake Wa Matarsa
  1. Ki riƙa ganin girman mijinki, saboda miji yana da haƙƙi mai girma a kan matarsa, saboda girman haƙƙin miji a kan matarsa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce: “Matar mutum ba ta taɓa cutar da shi a nan duniya, face sai matarsa daga cikin matan Aljannah ta ce: “Ki daina cutar da shi, Allah ya tsine maki, shi fa baƙo ne a wurinki, ya kusa ya rabu da ke ya zo wurinmu””. Ibn Majah 1857.
  2. Ki riƙa neman yardar mijinki, ki taimaka masa wajen neman halal, kada ki zama marowaciya ga ƴ an uwan miji, da sauran mutan gida, ki zamo mai taimaka masa wajen yi wa Allah ɗa’a a duk abin da ya umurce shi da abin da Allah ya hane shi, kada ki riƙa tuna masa kirkin mijinki na farko idan ke bazawara ce a wurinsa, kada ki fita daga gida sai da izininsa, kada ki tambaye shi zuwa unguwa ki haɗa da zuwa inda ba ki tambaye shi ba, kuma ki daina yawan fita unguwa in ba ta zama dole ba.
  3. Kada wani ya shigo gidan mijinki sai da izininsa, ki yi ƙoƙari wajen neman ilimi da aiki da shi, ki riƙa damuwa da kula da mijinki da nuna damuwa akan abin da ya dame shi na farin ciki ko akasin haka ga ƴ aƴ ansa har wanda ba ke kika haifa ba, kada ki riƙa bijiro da saɓani a gaban yara. Ki kasance mai yawan tsafta a cikin gidanki da jikinki.
  4. Ki riƙa girmama iyayen mijinki, musamman mahaifiyarsa ko da tana cutar da ke, da sauran ƴ an uwnsa da abokannensa, da sauran duk masu alaƙa da shi. Da kuma kawar da kai ga saɓanin da bai taka kara ya karya ba. Ki guje wa duk ƙawar da take ba ki shawarar ɗaukar fansa akan saɓa maki da aka yi.

Da kuma ƙawaye mazuga waɗanda ba za su baki shawara ta gari ba game da mijinki ko ƴ an uwan mijinki ko wani abu da ya shafi gidanki.

  1. Ki riƙa amsa kiransa a duk lokacin da ya buƙace ki zuwa shimfiɗa, ki guji yaɗa labarin yadda kuke kwanciya ga ƙawayenki. Ki guji kaɗaita da namijin da ba muharraminki ba.

Waɗannan kaɗan ne daga cikin muhimman abubuwan da ya kamata mace ta kiyaye su don ta tattali mijinta, kuma in Allah ya so duk matar da ta kiyaye waɗannan abubuwa za ta zauna lafiya da mijinta.

LABARAI MASU NASABA

EFCC Ta Ƙwato Kadarorin Naira Biliyan 500 A Ƙarƙashin Gwamnatin Tinubu – Shettima

Bayan Kauce Hanya, Jirgi Ya Afka Cikin Teku A Hong Kong 

Daga MUHAMMAD TUKUR JALINGO

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Hukumar EFCC Ta Tsare Wasu Jami’anta 10 Bisa Zargin Karkatar Da Kayan Aiki
Labarai

EFCC Ta Ƙwato Kadarorin Naira Biliyan 500 A Ƙarƙashin Gwamnatin Tinubu – Shettima

October 20, 2025
Bayan Kauce Hanya, Jirgi Ya Afka Cikin Teku A Hong Kong 
Labarai

Bayan Kauce Hanya, Jirgi Ya Afka Cikin Teku A Hong Kong 

October 20, 2025
Jami’an Tsaro Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar #FreeNnamdiKanuNow A Abuja
Labarai

Jami’an Tsaro Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar #FreeNnamdiKanuNow A Abuja

October 20, 2025
Next Post
Sin Da Amurka Na Iya Cimma Manyan Nasara Tare In Ji Shugaba Xi

Sin Da Amurka Na Iya Cimma Manyan Nasara Tare In Ji Shugaba Xi

LABARAI MASU NASABA

Hukumar EFCC Ta Tsare Wasu Jami’anta 10 Bisa Zargin Karkatar Da Kayan Aiki

EFCC Ta Ƙwato Kadarorin Naira Biliyan 500 A Ƙarƙashin Gwamnatin Tinubu – Shettima

October 20, 2025
Kano Pillars Ta Dakatar Da Manyan Masu Horas Da ‘Yan Wasanta Saboda Rashin Nasara

Kano Pillars Ta Dakatar Da Manyan Masu Horas Da ‘Yan Wasanta Saboda Rashin Nasara

October 20, 2025
Bayan Kauce Hanya, Jirgi Ya Afka Cikin Teku A Hong Kong 

Bayan Kauce Hanya, Jirgi Ya Afka Cikin Teku A Hong Kong 

October 20, 2025
Jami’an Tsaro Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar #FreeNnamdiKanuNow A Abuja

Jami’an Tsaro Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar #FreeNnamdiKanuNow A Abuja

October 20, 2025
Wani Mai Taɓin Hankali Ya Kashe Mutum 1, Ya Raunata 3 A Taraba

Wani Mai Taɓin Hankali Ya Kashe Mutum 1, Ya Raunata 3 A Taraba

October 20, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas

‘Yansanda Sun Kama Alburusai 400 A Delta

October 20, 2025
Kano Derby: Barau FC Ta Doke Kano Pillars A Karon Farko A Tarihin Gamuwarsu

Kano Derby: Barau FC Ta Doke Kano Pillars A Karon Farko A Tarihin Gamuwarsu

October 19, 2025
Binciken CGTN: An Fitar Da Sakamakon Jin Ra’ayin Jama’a Dangane Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Kolin JKS Na 20

Binciken CGTN: An Fitar Da Sakamakon Jin Ra’ayin Jama’a Dangane Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Kolin JKS Na 20

October 19, 2025
Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Muƙaman Gwamnatin Tinubu — Shugaban FCC

Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Muƙaman Gwamnatin Tinubu — Shugaban FCC

October 19, 2025
Xi Jinping Ya Mika Sakon Taya Cheng Li-wun Murnar Zama Shugabar Jam’iyyar KMT Ta Kasar Sin

Xi Jinping Ya Mika Sakon Taya Cheng Li-wun Murnar Zama Shugabar Jam’iyyar KMT Ta Kasar Sin

October 19, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.