Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis a Jaji da ke jihar Kaduna ya jinjina tare da irin sadaukarwa gami da nasarorin da dakarun sojin kasar nan suke samu wajen kare kasar nan da kuma jajircewarsu.
Da yake jawabi a wajen yaye dalibai 247 na manyan kwas 44 ta Kwalejin horar da jami’an soji da ke Jaji, shugaba ta cikin sanarwar da hadiminsa Garba Shehu ya fitar, Buhari ya sha alwashin cewa, gwamnatinsa za ta cigaba da samar wa dakarun Sojoji abubuwan da suke bukata na goyon baya wajen cigaba da yakar ‘yan ta’adda da ta’addanci.
‘‘Sojojin Nijeriya su na aiki tukuru da kwarewa da gogewar da suke da su wajen shafe barazanar tsaro da kare kasar nan.
“Kokarin sojojin kasa na yaki da ‘yan Boko Haram, ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane, da sauran matsalolin tsaro abun jinjina da yabawa ne. Tababs sojojin mu na kokari.
“Wannan Gwamnatin za ta ci gaba da samar da dukkanin abubuwan da Sojoji ke bukata da goya musu baya domin cimma nasarorin da aka sanya a gaba,” ya shaida.
Shugaban ya ce matsalolin tsaro da ake fama da shi a duniya baki daya ma na samo asali ne bisa dalilai daban-daban. Don haka ya ce akwai bukatar kara sanya tsaro a iyakokin kasar nan domin dakile aniyar ‘yan ta’adda.
Daga bisani ya taya wadanda aka yaye murna tare da jawo hankalinsu da su bada tasu gudunmawar wajen kare kasar nan a kowani lokaci.
A jawabinsa na maraba, Kwamandan Kwalejin, Air Vice Marshall (AVM) Olurotimi Tuwase, ya yi bayanin cewa sojoji 111 ne, 69 sojojin ruwa ne, 42 kuma Sojoji sama ne, da kuma wasu karin daliban da aka yaye da suka samu horo daban-daban ciki har da dalibai daga kasashen waje.
AVM Tuwase ya kara da cewa, daliban da aka yaye kan kwas din 44 sun fito daga kasashen Burkina Faso, Cameroun, Chad, The Gambia, Ghana, Liberia, Mali, Niger, Rwanda, Sierra Leone, Tanzania, Togo da Zambia.
Kwamandan ya gode wa shugaban kasa Buhari a bisa irin goyon bayan da yake basu da karfafawa musu guiwa a kowani lokaci.
A wajen taron Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika lambar yabo ga daliban da suka yi zarra a cikin wadanda aka yaye din.